Buratai: Zamu saki bayanai kan bincikar Janar Danjuma TY da muke yi kowa ya gani

Buratai: Zamu saki bayanai kan bincikar Janar Danjuma TY da muke yi kowa ya gani

- TY Danjuma ya barota a makonnin baya, ya zargi sojda kisan kare-dangi

- Sojojin sunce zasu bincike shi kuma zasu bayyana abin da suka tono

- Jihar Benue ta zama jihar kashe-kashe tsakanin manoma da makiyaya

Buratai: Zamu saki bayanai kan bincikar Janar Danjuma TY da muke yi kowa ya gani
Buratai: Zamu saki bayanai kan bincikar Janar Danjuma TY da muke yi kowa ya gani

A ranar Larabar nan ne shugaban rundunar sojin Najeriya, Lt. General Tukur Buratai, yace rundunar zata sanar da sakamakon binciken data gabatar akan zargin da ake yi na cewa akwai sa hannun rundunar sojin a rikicin makiyaya da ake yi a jihar Taraba, kamar yadda T.Y Danjuma ya ce.

Buratai wanda yayi magana a lokacin da kwamitin take taro, inda shugaban taron Manjo Janar Joseph Nimyel, ya gabatar da rahoton sa a gaban kwamiti, yayinda yake tabbatar da cewar rundunar zata saki sakamakon binciken da ta gabatar ga jama'a domin su yanke hukunci akan zargin.

Bayan haka kuma a wurin wannan taron, shugaban rundunar sojin ya kafa kwamiti wanda zasu tabbatar da ingancin makamai, da kuma hanyar da aka bi aka mallakesu. Da yake karbar rahoton jihar Taraban, Buratai ya ce;

"Zamu dauki wannan bincike da matukar muhimmanci, sannan kuma zamu sannar da manyan hukumomi wadanda ya kamata su san gaskiyar abinda ke wakana."

Bayan haka kuma zamu bada rahoto ga kafafen yada labarai, domin su fahimtar da jama'a gaskiyar abinda yake faruwa akan zargin da ake yiwa rundunar sojin Najeriyan.

Buratai yace fitar da rahoton ga jama'a yana da matukar muhimmanci domin su san gaskiyar abinda ke afkuwa a yankin, sannan ya kuma ya godewa kwamitin da irin kokarin da suka nuna. Ya kuma bukaci kwamitin data tabbatar da gaskiya a cikin binciken ta.

DUBA WANNAN: Rigimar Larai da Turai: Iran ta mayar wa da Saudiyya martani

Da yake karbar rahoton kwamitin daya kafa domin tantance inganci da kuma yawan makaman da rundunar sojin ta mallaka, Buratai ya bayyana cewar dalilin da yasa aka kafa kwamitin shine, saboda yawan yaduwar makamai wanda ba a da takamaiman hanyar da suke shigowa.

Tabbatar da ingancin makamai ba abu bane mai sauki kamar yanda mutane suke tunani, amma duk da haka zamu yi kokari domin ganin mun tabbatar da ingancin dukkanin makaman da suke shigowa kasar nan, musamman ma a yanzu da yawan makaman yake ta faman karuwa a kasar nan..

Wannan matakin da muka dauka shine zai taimaka mana mu gano inda makaman suke fitowa, sannan zamu nemi hanyar da zamu bi domin magance matsalar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel