Kiristoci zasu gudanar da zanga-zanga sakamakon kashe-kashen da ake a jihar Benue

Kiristoci zasu gudanar da zanga-zanga sakamakon kashe-kashen da ake a jihar Benue

- Hakurinmu na neman karewa inji kungiyar CAN

- Kungiyar CAN ta ce, zata gudanar da zanga-zangar lumana ta kasa baki daya

- A wannan ranar kuma a gudanar da addu'o'i na musamman domin daliba daya yar Dapchi kirista da ba'a sako ba

Kungiyar Kirisotocita kasa (CAN) tayi kira ga duk ilahirin Kiristocin Najeriya da su shirya gudanar da zanga-zanga domin nuna alhininsu game da kiyashin da Makiyaya yan ta’adda ke yiwa al’ummar jihar Benue ba kakkautawa.

Kiristoci zasu gudanar da zanga-zanga sakamakon kashe-kashen da ake a jihar Benue
Kiristoci zasu gudanar da zanga-zanga sakamakon kashe-kashen da ake a jihar Benue

A wani jawabi da Adebayo Oladeji, mataimaki na musamman kan yada labarai ga shugaban kungiyar (CAN) ta kasa Samson Ayokunle, ya gabatar yace, yawaitar kashe-kashen abin takaici ne da damuwa da yake nuna cewa Najeriya na shirin komawa kamar ba doka.

Da sanyin safiyar yau ma dai wasu mahara sun afkawa jihar ta Benue inda suka kai hari Cocin Saint Ignatius Catholic in da har Mutane 19 suka rasa ransu ciki harda manyan limaman cocin.

Zanga-zangar dai da za'a sanar da ranar gudanarwar nan gaba, za’a fara ne domin jan hankalin gwamnati ta kara daukara matakan ceto kirista guda da ta rage da kuma 'yan Matan Chibok da Boko Haram suka dauke da sauran wadanda 'yan ta'adda suka kame a ko’ina. A cewar mataimakin shugaban kungiyar.

An sha dai kai hare-hare a jihar ta Benue da kewayenta wanda yayi sanadiyyar mutawa da jikkata Mutane da dama. Harin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da shi.

Yayin zanga-zangar dai ana saran Kiristocin zasu na daddaga kwalaye dauke da rubutun da ke nuni da rashin jin dadinsu da matsalar rashin tsaron kamar; Ya ishe mu haka, kisan gillar ya isa, gwamnati tasa a saki Sharibu, kisan da makiyaya suke dole ne a daina da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel