Babu bata yi ba: An kai wasu Matasa 5 kotu bayan satar taliya da katin waya

Babu bata yi ba: An kai wasu Matasa 5 kotu bayan satar taliya da katin waya

- Dubun wasu samari ta ciki, bayan da yan sanda suka cafke su

- Hausawa kan ce rana dubu ta barawa guda kuma ta mai kaya.

An gurfanar da wsu samari su 5 da suka haura shagon wani mai kanti gaban kotun mai shari’a Magistrate O. Sule-Amzat dake garin Lagos yau Laraba.

Samarin dai sun haura ne ta saman rufin shagon kuma su kayi awon gaba da kayan da darajarsa ta kai N308, 000,

Samarin da aka bayyana sunansu da; Damilare Omoniyi mai shekaru 19 da Adedayo Shodipo 20, da Idris Abubakar 23, da Olamide Adedimeji 18, da kuma Tolani Nasri 22 dukkanninsu mazauna unguwar Oshodi ta jihar Lagos.

KU KARANTA: Tsaka mai wuya: An fara tantance saka hannun masu son yiwa Dino Melaye kiranye

Jami’in dan sanda Sufeto Benson Emuerhi ya shaidawa kotun cewa, samarin sun haura shagon Mutumin mai suna John Ezeka, suka dauki katin waya da katan din taliyar Indomie da kudinsu ya kai N223, 000, sanna kuma suka dauki kudi har Naira Naira N85, 000.

Babu bata yi ba: An kai wasu Matasa 5 kotu bayan satar taliya da katin waya
Babu bata yi ba: An kai wasu Matasa 5 kotu bayan satar taliya da katin waya
Asali: UGC

Dan sandan yace sun aikata laifin ne tun ranar 17 ga watan Afrilu a unguwa mai lamba 1 dake unguwar Edu St., Mafoluku ta Oshodi, a Lagos. Kuma ana zargin su ne da laifuka har guda uku; Sata da haura gida da kuma karbar kayan sata.

“Sun haura shagon mai kayan ne ta saman silin, masu gadi sun bi su amma basu samu damar kama su ba. Kafin daga bisani jami’an yan sanda su yi nasar cafke su.a unguwar Mafoluku." inji Sufeton yan sandan.

A cewar Dan sanda mai kara, guda daga cikin wadanda ake zargin yana sane da cewa sunyi satar amma ya rinka karbar Naira dubu biyu daga kowannensu.

Laifukan da suka aikata dai ya saba da kudin dokar manyan laifuka ta jihar Lagos karkashin sashi na 287 da 309 da 411 na shekarar 2015.

Sai dai kuma dukkannin wadanda ake zargin sun ki amsa laifin.

Daga karshe alkalin ya bayar da belinsu akan kudi Naira 100,000 kowannensu da kuma kawo wadanda zasu tsaya musu mutukar suna da gida da aiki a jihar ta Lagos, sannan kuma su kawo takardar shaidar biyan haraji ta shekaru biyu.

Idan kuma basu cika sharuddan ba, sai a iza keyarsu zuwa gidan maza har sai ranar 23 ga watan Yuli kafin su dawo kutun don yane hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel