Waiwayen tarihi: Gobaran da ya faru a Hajjin 1997, akalla mutane 300 suka hallaka

Waiwayen tarihi: Gobaran da ya faru a Hajjin 1997, akalla mutane 300 suka hallaka

A ranan 16 ga watan Afrilu, 1997, wani mumunan hadarin gobara ya faru yayinda ake gudanar da aikin hajji wanda ake siffantawa da daya daga cikin manyan haduran da suka faru a tarihin aikin hajji.

Yayinda aikin Ibadan ke gudanar, wani wuri ya cinkushe da dubunnan mutane inda da dama suka rasa rayukansu.

Wannan gobara ya faru ne sanadiyar fashewan iskar Gas da daya daga cikin mahajjata ya kawo tantin mahajjata domin yin girki.

Waiwayen tarihi: Gobaran da ya faru a Hajjin 1997, akalla mutane 300 suka hallaka
Waiwayen tarihi: Gobaran da ya faru a Hajjin 1997, akalla mutane 300 suka hallaka

Da farko, wuta ta kama rumfa daya amma kafin ka sani sauran rumfan suka dauka. Sakamakon haka kimanin rumfuna 70,000 ne suke kone.

KU KARANTA: Shekaru 12 bayan kisan Saddam Hussein, ina gawarsa take?

Game da cewar hukumar Saudiyya, mutane 217 sun rasa rayukansu amma 1290 ne suka jikkata, amma idanuwan shaida da manema labarai sun ce akalla 300 ne suka mutu.

Allah ya kiyaye gaba, Amin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel