Cin amana ruwa ruwa: Wasu mutane 4 sun zakke ma yayan wani abokinsu guda 2

Cin amana ruwa ruwa: Wasu mutane 4 sun zakke ma yayan wani abokinsu guda 2

Wasu dattijon biri su hudu dake aiki da kamfanin Kazmus Nig Ltd. sun zakke ma wasu yara mata guda biyu yayan wani abokin aikinsu, inji rahoton jaridar The Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an gurfanar da masu laifin a gaban kuliya manta sabo, wata Kotun hukunta laifukan da suka shafi fyade da ci zarafin mata, dake zamanta a Ikeja na jihar Legas, kan tuhumarsu da yi ma yara mata biyu fyade masu shekaru 3 da 5.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta’addan Boko Haram, sun ceto mutane da dama

Mutanen da ake tuhuma sun hada da direban kamfanin, Ojo Taiye mai shekaru 35, maigadin kamfanin John Mohasan mai shekaru 24, Adenekan Adedeji mai shekaru 40 da kuma Peter Arabo mai shekaru 33, kuma suna fuskantar tuhume tuhumen da suka shafi fyade da da cinz zarafi, sai dais u musanta laifin.

Cin amana ruwa ruwa: Wasu mutane 4 sun zakke ma yayan wani abokinsu guda 2
Yannn

Lauya mai kara, I.Solarin ta bayyana ma Kotu cewa a watan Nuwambar shekarar 2015 ne mutanen suka tafka wannan ta’asa a shagon aikinsu dake titin Fagbu-Iju dake unguwar Agege, inda tace yaran sun tabbatar da cewa mutanen sun dade suna zakke musu.

“Haka zalika a lokutta da dama sukan sanya al’aurarsu a bakin yarinyar mai shekaru 5, hakan na faruwa ne sakamakon yaran su na jiran mahaifinsu a wajen aikinsa bayan sun tashi daga makaranta, daga nan sai ya wuce dasu gida, don haka suke zakke ma yaran a duk lokacin da mahaifin ya bar wajen.” Inji lauya.

Asirin mutanen ya tonu ne a lokacin da guda cikin yaran ta bayyana ma mahaifinta cewar tana jin zafi a al’aurarta, daga nan ya fara binciken dalilin zafin, inda ya gano ashe dayar yar tasa ma na fama da wannan matsala.

Bayan sauraron lauya mai shigar da kara, Mai shari’a Nwaka ta dage sauraron karar,sa’annan ta bada umarnin a garkame mata wadanda ake zargin a Kurkuku, har zuwa ranar cigaba da sauraron karar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng