Shekaru 12 bayan kisan Saddam Hussein, ina gawarsa take?

Shekaru 12 bayan kisan Saddam Hussein, ina gawarsa take?

Saddam Hussein ya shugabanci kasar Iraqi daga shekarar 1979 zuwa 2013. ya kasance daya daga cikin manyan shugabannin da suka shugabanci kasar a tarihin Iraqi.

Wata kotu a kasar Iraqi ta yankewa Saddam hukuncin kisa kan laifin kashe yan Shi’a kimanin 148.

A ranan 30 ga watan Disamba, an rataye Saddam Hussein kuma aka tafi da gawarsa ranan 31 ga watan zuwa mahaifarsa Al Awjah.

Da aka kai gawarsa, kabilarsa ta Albu Naseer ta amince da cewa a birne gawar Saddam Hussein ba tare bata lokaci ba.

Amma yanzu akwai jita-jitan cewa an dauke gawar Saddam Hussein daga kabarinsa. Wasu sun ce ma ba’a ratayesa ba, shin me gaskiyan?.

Shekaru 12 bayan kisan Saddam Hussein, ina gawarsa take?
Shekaru 12 bayan kisan Saddam Hussein, ina gawarsa take?

Yan Shi’a karkashin gamayyar Hashad Al-Shaabi sun ruguza gidan da aka birne Saddam Hussein kuma ana sa ran an tona kabarinsa an dauke gawarsa.

Wasu sunce diyar Saddam Hussein Hala ta dauke gawar mahaifinta kuma ta tafi da shi lasar Jordan, amma wani babban farfesa wanda dalibin Saddam Hussain ne ya musanta hakan saboda diyar Saddam bata sake dawowa kasar Iraqi ba.

KU KARANTA: Ina da masu zuwa yawo, za'a mayar da dajin Sambisa wurin buɗe idanu

Amma har yanzu, babu wanda ya san inda gawar take ba. Amma dai wasu na cewa harin Bam din da aka kai ya tarwatsa gawar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel