Sabon bincike: Rashin cin abincin safe zai iya sanya kiba da kuma girman kugu
- Ina masu son yin kiba? ga sabuwar hanya sai a gwada
- A zauna da yunwa har sai lokacin cin abincin rana kafin a ci komai tun safe
Wani sabon bincike da aka gudanar a kasar Amurka ya bayyana cewa, akwai yiwuwar mutanen da suke tsallake karin kumallo na iya kara nauyinsu da kuma samun kugu mai girma.
Binciken da Kevin Smith daga Mayo Clinic ya jagoranta an dai wallafa shi ne a yanar gizo. Binciken ya nuna cewa, kaso 26.7% na mutane da suke tsallake cin abincin safe masu kiba ne sosai idan aka kwatanta da 10.9% na wadanda da suke karyawa kullum.
Haka zalika, wadanda basa karyawa gaba daya kullum, sun kai rahoton karuwar kibar sosai a shekara da ta gabata.
KU KARANTA: Wani limami 'dan Najeriya ya tsinci kudi mai yawa a Saudiyya, ya mayar dasu saboda tsoron Allah
An dai yiwa binciken lakabi ne da "karyawa akai-akai da kuma karuwar kiba da nauyi" (Frequency of Breakfast Consumption, Obesity and Weight Gain).
Binciken ya gudana ne tsakanin Mutane 347 yan rukunin shekaru 18 - 87, daga Shekara ta 2015 zuwa 2017.
Kuma binciken ya nuna cewa, wadanda suke kin cin abincin safe sun samu karin Kugu mai girman 97.5 cm, fiye da wadanda suke karyawa kullum da suka samu 9.8 cm.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng