Gwamnatin jihar Bauchi ta bayar da hutu sakamakon ziyarar da shugaba Buhari zai kai a jihar
- Shugaba Buhari zai kai ziyarar kwanaki biyu a jihar Bauchi
- Shugaban kasar zai isa garin Bauchi a gobe Alhamis 26 ga Afirilu
- Gwamnatin jihar ta Bauchi ta bayar da hutu gabanin zuwan shugaban kasar
Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na jihar Bauchi ya bayar da hutu a gobe Alhamis 26 ga watan Afirilu, gabanin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kwanaki biyu a jihar.
A wani bayani da Mr Ali Ali, babban mai bawa gwamnan shawara gameda sadarwa ya turowa Legit.ng, yace hutun an bayar dashi ne domin ayi shirye shiryen gagarumar walima ga shugaban kasar a gobe.
Shuban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka a jihar musamman na hanyoyi da kuma rabon motocin noma guda 500 ga manoma na jihar.
KU KARANTA KUMA: Sanatoci sunyi fada akan binciken EFCC da takewa Sanatocin
Gwamnan ya bukaci mutanen jihar dasu fito kwansu da kwalkwata don suyiwa shugaban kasar sannu da zuwa idan ya isa jihar.
A halin da ake ciki, John Odigie-Oyegun, ciyaman na Jam’iyyar APC na kasa ya bayyana cewa bukatar masu fada aji na jam’iyyar ta APC na cewa Oshiomole ya gaji kujerarsa yarinta ne.
Odigie-Oyegun yace ya gama shawara da wadanda zaiyi saboda haka zai bayyana shawarar da ya yanke game da sake tsayawa takara a matsayin ciyaman na jam’iyyar nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng