Karar kwana: Mutane da yawa sun bakunci lahira sakamakon girgizar kasa

Karar kwana: Mutane da yawa sun bakunci lahira sakamakon girgizar kasa

- Kwanan wasu mutane ya kare a dalilin afkuwar girgizar kasa da ta faru a kasar Turkiyya

-Bayan Mutane lamarin ya ritsa har da dabbobi

Mahukuntar kasar Turkiyya sun tabbatar da mutuwar mutane da dama a dalilin afkuwar wata yar girgizar kasa a kudancin kasar.

Karar kwana: Mutane da yawa sun bakunci lahira sakamakon girgizar kasa
Karar kwana: Mutane da yawa sun bakunci lahira sakamakon girgizar kasa

Girgizar kasar dai ta faru ne a kauyen dake alkaryar Adiyaman da sanyin safiyar jiya Talata da misalin karfe 3:34 na safe.

Binciken da masana kasa a kasar Amurka su kayi ya nuna cewa, karfin girgizar kasar ya kai mizanin 5.2 dake da karfin yin zurfi har na tsawon kilomita 10 a cikin kasa.

KU KARANTA: Fasaha: Wani matashi a Najeriya ya kirkiro inji mai samar da wutar lantarki da bokitin ruwa

Ministan lafiya na kasar ta Turkiyya ya shaida cewa, har yanzu akwai kimanin Mutane 35 da suke karbar magani a dalilin raunin da suka ji sanadiyyar tsorata da kuma yunkurin guduwa domin tseratar da rayuwarsu.

Wata majiyyaciya Zeynep Berk, da bangorin gida ya fadowa tare da wasu karin wasu Mutane hudu, ta ce, da kyar aka samu aka ceto su sannan kuma aka koma domin ceto dabbobinsu kimanin 150. Kamar yadda jarida Independen ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng