Dodanni sun kar farmaki a wani wurin ibada, sun kashe jama'a da dama
Mahukunta a rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Anambra sun sanar da samun nasarar da suka yi akan wasu dodanni da suka hargitsa ayyukan ibada a wata majami'ar dake a karamar hukumar Idemili ta yamma a ranar Juma'ar da ta gabata da dare.
Jami'ar hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan ne dai Nkeiruka Nwode ta shaidawa manema labarai hakan a garin Awka, babban birnin jihar.
KU KARANTA: Yakubu Gowon ya caccaki Buhari a kaikaice
Legit.ng ta samu cewa Uwar gida Nkeiruka Nwode ta kuma kara da cewa jami'an su sun samu nasarar kama wasu uku daga cikin dodannin kuma tuni ma har bincike a kan su yayi nisa.
A wani labarin kuma, Daya daga cikin tsaffin shugabannin kasar Najeriya a mulki soja Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya bayyana damuwa da kuma takaicin yadda yace harkokin tsaro na ta dada kara tabarbarewa a sassan kasar nan.
Shi dai Gowon yayi wannan bayanin ne a yayin da ya halarci wani muhimmin taron addu'a ta musamman a garin Yanagoa, babban birnin jihar Bayelsa da ke zaman jihar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng