Fasaha: Wani matashi a Najeriya ya kirkiro inji mai samar da wutar lantarki da bokitin ruwa
Wani matashi dan Najeriya kuma injiniya mai fasaha daga jihar Kalaba wanda ake kira da suna Ogar Augustine Otuokwa ya baza ilimin sa inda ya kirkiro wani injin da ke samar da wutar lantarki daga bokitin ruwa.
KU KARANTA: Buratai ya muhimmin roko ga sojojin Najeriya
Kamar dai yadda muka samu, matashin ya bayyana cewa injin samar da wutar lantarkin na shi yana samar da wutar da ta kai ma'aunin Watt 20 wanda wannan din ya ishe shi ya rika caza wayoyin salula da.
Legit.ng ta samu cewa Ogar Augustine Otuokwa kwararren injiniya ne da ya kammala karatun sa daga jami'ar garin Kalaba kuma ya fito ne daga kauyen Wula dake a karamar hukumar Boki ta jihar Kuros Ribas.
Da yake karin haske game da fasahar ta sa, matashin da yanzu haka aka bayyana adadin shekarun sa a 32 ya dauki tsawon lokaci yana yi wa 'yan jarida yadda injin din na sa yake aiki sannan kuma ya bukaci gudummuwa daga gwamnati.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng