Hukumar Hisba ta gano wasu masu bautar bishiya a jihar Kano

Hukumar Hisba ta gano wasu masu bautar bishiya a jihar Kano

Kamar dai yadda majiyar mu ta Rariya ta bankado, jami'an hukumar nan dake tabbatar da da'a da gyaran tarbiyya ta jihar Kano watau Hisbah ta gano wasu mutane da ta zargi suna bautawa wata bishiya tare da kuma da sare ta a jihar Kano.

Hukumar Hisba ta gano wasu masu bautar bishiya a jihar Kano
Hukumar Hisba ta gano wasu masu bautar bishiya a jihar Kano

KU KARANTA: Gaskiya daya ce: Fashola ya fallasa inda Buhari bai aiki

Mun samu dai cewa wannan abin al'ajabin an ce ya faru ne a wani kauyen da ake kira da suna 'Dorawar Tazalli' a can karamar hukumar Kunci ta jihar Kano din inda aka zargi wasu mutane da tarewa a gindin wata bishiya suna zuba ruwa a jikinta suna sha da nufin warkewa daga cutuka.

Legit.ng haka zalika ta samu cewa wasun su ma kuma har suna zazzagaya bishiyar a wani salo da ke yanayi da dawafi da ake yi wa dakin Ka'aba.

Shugaban hukumar ta Hisba dai ya tabbatar da aukuwar labarin sannan kuma ce tuni jami'an su sun sare bishiyar saboda gudun kar ta rikide ta koma wajan bauta tare kuma da yin kira ga Malamai da su dinga shiga kauyuka domin fadakar da jama'a.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng