Yakubu Gowon ya caccaki Shugaba Muhammadu Buhari a kaikaice
Daya daga cikin tsaffin shugabannin kasar Najeriya a mulki soja Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya bayyana damuwa da kuma takaicin yadda yace harkokin tsaro na ta dada kara tabarbarewa a sassan kasar nan.
Shi dai Gowon yayi wannan bayanin ne a yayin da ya halarci wani muhimmin taron addu'a ta musamman a garin Yanagoa, babban birnin jihar Bayelsa da ke zaman jihar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
KU KARANTA: An yi yunkurin juyin mulki a Saudiyya
Legit.ng ta samu kuma haka zalika cewa Gowon din ya bayyana karin samun hare-hare daga 'yan Boko Haram da makiyaya da ma barayi da masu sace mutane a matsayin babban abun damuwa a kasar nan.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Imo dake a shiyyar kudu maso gabashin kasar nan kuma shugaban gwamnonin jahohin Najeriya karkashin jam'iyyar APC Mista Rochas Okorocha a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana cewa dukkan su sun bayyana goyon bayan su ga tazarcen shugaba Buhari.
Gwamna Okorocha yayi wannan bayanin ne ga 'yan jaridar fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya jagoranci takwarorin sa zuwa wata ganawa da suka yi da shugaba Buhari din a fadar sa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng