Ina da masu zuwa yawo, za'a mayar da dajin Sambisa wurin buɗe idanu

Ina da masu zuwa yawo, za'a mayar da dajin Sambisa wurin buɗe idanu

- Ga masu mafarkin zuwa ganin dajin Sambisa, lokaci ya karato sai a shirya

- Nan da wani lokaci za'a mayar da dajin sambisa wajen yawon bude ido

- Yusuf Buratai ne ya fadi yunkurin rundunar Sojojin Abuja

Bababan hamsan Sojojin ƙasar nan, Janar Tukur Buratai ya ce, rundunar sojin zata haɗa hannu da gwamnati da kuma hukumar gandun daji da wuraren shakatawa ta jihar Borno, don ganin an kimtsa ƙasurgumin dajin nan na sambisa yadda zai yi kyau domin jan hankalin masu son ƙara samun ilimi da kuma ganin ganin kwakwaf.

Ina da masu zuwa yawo, za'a mayar da dajin Sambisa wurin buɗe idanu
Ina da masu zuwa yawo, za'a mayar da dajin Sambisa wurin buɗe idanu

Buratai dai ya faɗi hakan ne a jiya Talata yayin da ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar wuraren shaƙatawa ta ƙasa Ibrahim Goni, a babbar shelkwatar tsaro ta ƙasa dake Abuja.

KU KARANTA: Melaye ya shiga uku, yan sanda 30 sun bi shi har gadon asibiti sun sake kama sa

Dajin na Sambisa na Kudu maso yammacin wurin shaƙatawa na yakin kogin Chadi, kimanin kilo mita 60 zuwa cikin babban birnin jihar Borno.

Yanzu haka dai sojojin Najeriyar ne suke ta aikin gina tituna da hanyoyi a cikin dajin Sambisan.

A cewarsa, sojojin sun gano dajin na Sambisar na da namun daji masu yawa sosai don haka suke neman haɗin gwuiwa da hukumomin da abin ya shafa wajen raya dajin.

A nasa jawabin Ibrahim Goni, ya ce, maƙasudin ziyarar tasa shi ne domin ganawa da Sojojin ya kuma shaida masu muhimmancin dajin ga tattalin arziƙi da kuma tsaron ƙasar nan.

Ina da masu zuwa yawo, za'a mayar da dajin Sambisa wurin buɗe idanu
Ina da masu zuwa yawo, za'a mayar da dajin Sambisa wurin buɗe idanu

Ya kuma ƙara da cewa, mafi yawancin gandun dajin ƙasar nan na fuskantar matsala a dalilin yaƙi da Sojojin ke yi da ƴan ta'adda, wanda hakan kuma barazana ne ga samuwar kuɗaɗen shiga ta fannin

Rundunar Sojojin ta dai rasa dakarunta 3 a wani artabu da su kayi da ƴan Boko Haran yayin da suka ɓankaɗo maɓoyarsu har guda 13.

A dalilin haka ne Goni ya yi ƙira da a matsa ƙaimi wurin horas da dakarun rundunar da kuma wadata su da kayan aikin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel