Melaye ya shiga uku, yan sanda 30 sun bi shi har gadon asibiti sun sake kama sa

Melaye ya shiga uku, yan sanda 30 sun bi shi har gadon asibiti sun sake kama sa

- Da alamu tsugunno bai karewa Dino melaye ba, yanzu haka duk da yana asibiti an sake kama shi

'Yan sanda cikin cikakken shirin ko ta kwana kimanin 30 ne su kayi dirar mikiya a asibitin Zankili Medical Centre dake Abuja, inda aka kwantar da Sanatan jihar Kogi ta yamma Sanata Dino Melaye.

Yanzu yanzu: Melaye ya shiga uku, yan sanda 30 sun bi shi har gadon asibiti sun sake kama sa
Yanzu yanzu: Melaye ya shiga uku, yan sanda 30 sun bi shi har gadon asibiti sun sake kama sa

An dai kwantar da shi ne, sakamakon dirowa da yayi daga motar da take dauke da shi don kai shi garin Lokoja.

lamarin kama shin dai ya biyo bayan kashin kaji da wasu da aka kama da aikata muggan laifuka su kayi, su kace shi ma mambansu ne, yayin da shi kuma ya karya ta hakan.

Rundunar yan sanda kuma ana ta barin ke son rabe Aya da tsakuwa.

KU KARANTA:

Da farko dai rundunar yan sanda reshen jihar Kogi ta fara aike masa da sammaci shi kuma Dino Melayen yaki amsa gayyatar, a sakamakpon haka rundunar ta yi masa kamun kazar kuku.

An dai rawaito cewa yan sandan da suka je sake kama shin na sanye ne da kayan ko ta kwana kamar zasu je kamo wani rikakken dan fashi da makami, kuma babban kakakin rundunar na kasa gaba daya ne ke jagorantar su Jimoh Moshood.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng