Murna baki har kunne: Darajar Naira ta ɗaga
- Yan Najeriya zasu dara, sakamakon dala ta fara ruguzowa
- Dalar dai ta fara karyewa ne kasuwar hada-hada tun jiya
Darajar Naira ta sake ɗagawa a kasuwar a kasuwar canji. Farashin Dalar $1 dai a yau Talata ana canza ta ne a kan Naira 360.
Kimanin kwanaki biyar ana canza Dalar akan Naira 360.54, kafin yau ta samu dagawa zuwa $1 kan Naira 360
Kasuwar hada-hadar ta shi ana canza Pound Sterling na ƙasar Ingila kan N510 yayin da ake canzar da Euro kan Naira N445.
Ƴan kasuwar canjin ƙudin dai sun bayyana jin daɗinsu ganin yadda Nairar ke cigaba da farfaɗawo daga danniyar da Dalar Amurka tayi mata.
KU KARANTA: Majalisa ta kafa kungiya ta musamman sakamakon harinda aka kai mata
Wasu da suka tofa albarkacin bakinsu sun ce, akwai yiwuwar Dalar ta sake faduwa sakamakon ƙaruwar rarar ƙuɗin da Najeriya ke ajiyewa a ƙasashen ketare da kuma kuɗaden da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare suka turo gida da darajarsa ta kai har biliyan 22b.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng