Da dumi-dumi: Ƴan sanda sun tarkata Melaye da komatsansa zasu hada shi da gaggan ƴan ta'adda a Lokoja

Da dumi-dumi: Ƴan sanda sun tarkata Melaye da komatsansa zasu hada shi da gaggan ƴan ta'adda a Lokoja

- Dino Malaye na cikin tsaka mai wuya, sakamakon samun wasu bayanai da suke nuni da cewar yana da hannu cikin aikata miyagun laifuka

- Tun jiya ne dai aka fara tsare shi a filin sauka da tashin jiragen sama kana yau da safe kuma ya mika kansa ga jami'an yan sanda

Sanatan Kogi ta yamma Dino Melaye, wanda ƴan sanda na sashin manyan laifuka (FSARS) suka kama a safiyar yau Talata,yanzu haka sun iza keyarsa zuwa garin Lokoja dake jihar Kogi.

Da dumi-dumi: Ƴan sanda sun tarkata Melaye da komatsansa zasu hada shi da gaggan ƴan ta'adda a Lokoja
Da dumi-dumi: Ƴan sanda sun tarkata Melaye da komatsansa zasu hada shi da gaggan ƴan ta'adda a Lokoja

Ana dai sa rai da zarar an kai shi ne za'a kuma haɗa shi cikin gungun waɗanda ake zargi da aikata manyan laifuka, domin sun ce shima mambansu ne, wanda hakan ya janyo jami'an ƴan sandan su kai ram da shi domin ba wanda da yafi ƙarfin doka.

KU KARANTA: Karanta domin sanin amfanin Citta 7 wanda yakamata kowa ya sani har dakai

Wata majiya dai ta bayyana cewa da farko an fara tsare Melaye ne a ofishin jami'an FSARS ɗin ne dake garin Abuja kusa da babban bankin ƙasa CBN, kafin da misalin karfe 12 rana su hau hanyar zuwa Lokojan cikin manyan motocin rundunar dake maƙare da jami'an ƴan sandan cikin shirin ko ta kwana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel