Da naso da tuni na zama shugaban kasa inji Atiku
- Atiku ya bayyana cewa, maganar yana son na zama shugaban kasa ta kowanne hali ba gaskiya bace
- Ya kuma ce, Abiola ma shi ya janye masa takarar cikin gida ta fidda gwani da akai zabe lokacin Babangida
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, bayyana cewa, da yaso da tuni ya zama shugaban kasa.
Amma sakamakon yana kishin ganin cigaban hadin kan Najeriya yasa ya hakura da bukatar tasa.
Da yake zantawa da BBC Hausa, a garin Kaduna a yau Talata, Atiku ya ce, a shekarar 1992 ya janyewa MKO Abiola takara zaben fidda gwani na jam’iyyar SDP, duk kuwa da cewa alamu sun nuna zai iya samun nasara.
Haka zalika 1 shekarar 2003 ya bijirewa sha’awar da wasu gwamnoni suka nuna sha’awarsu na yayi takara zasu goya masa baya, amma sai ya zabi kada ya ci amanar ubangidansa Shugaban kasa na wancan lokaci Obasanjo.
A saboda haka ne Wazirin Adamawan ya soki lamarin wadanda suke tunanin ya kagu ya zama shugaban kasa ta kowanne hali, domin a cewarsa da hakan zargin nasu yake, to da bai janyewa Abiola da kuma cigaba da bin Obasanjo ba.
KU KARANTA:
Da yake amsa tambayar ko menene dalilin da yasa yake son ya zama shugaban kasa kuwa, Atiku ya ce, Shi da yayi shekaru takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa, kuma da yadda abubuwa suke tafiya a hilin yunzu bangaren tattalin arziki, yana da gogewar da zai iya fitar da A’i daga rogo.
ya kuma kara da cewa, a yadda tsarin cajin kudin kasashen waje yake musamman dala, babu wani mai zuba hannun jari da zai zo Najeriya domin rashin tartibiyar manhajar canji guda.
Ga matasa ba aiki, don haka in na samu damar shugabatar Najeriya, samarwa da matasa aikin yi shi zan mayar da hankali sosai, kuma zan iya don kowa yaga yadda na kafa kamfanunuwa daban-daban a kasar nan.
wadannan sune abubuwan da nake son na samu damar gyarawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng