BigBrotherNaija: Ko menene alfanunsa da har ake ta rububinsa haka tsakaniin samari

BigBrotherNaija: Ko menene alfanunsa da har ake ta rububinsa haka tsakaniin samari

- Shirin big brother Naija ya hada Naira biliyan biyar

Shirin big brother Naija kashi na uku da aka kammala mai taken "Double wahala" ya hada Naira biliyan 5.1 daga masu kallo

- Ko menene alanunsa ga rayuwarmu?

BigBrotherNaija: Ko menene alfanunsa da har ake ta rububinsa haka tsakaniin samari
BigBrotherNaija: Ko menene alfanunsa da har ake ta rububinsa haka tsakaniin samari

Shirin big brother Naija kashi na uku da aka kammala mai taken "Double wahala" ya hada Naira biliyan 5.1 daga masu kallo, a ittifakin PREMIUM TIMES.

Mai masaukin shirin, Ebuka Obi ya bayyana cewa sama da kuri'u miliyan 170 aka samu a lokacin da ake shirin, miliyan 30 aka samu a satin karshe.

Yanda wasan Big Brother Naija din yake, za a ce ma masu kallo da su sa ma wadanda suka fi birgesu a gidan. Masu kuri'u mafi yawa su suka ci gasar.

Wannan ya nuna cewa shirin ya samu Naira biliyan 5.1 daga masu kallo kadai da kashi 17.6 (N900 million) yazo a satin karshe.

Idan aka danganta da kuri'u da aka samu, wanda yayi nasara ya tafi da kashi 0.88 cikin dari(N45 miliyan). Wannan ya nuna cewa mashiryan shirin sun samu riba sosai da shirin.

Sai dai bbu wani alfanu banda kasuwanci da shirin ke koyar da samari, banda son kallon batsa, lalata, lalaci da cima-zaune. Kudaden kuma da aka hada, biliyoyi, an kwashe su an kai Afirka ta kudu.

N25m ce kadai zata shiga hannun wanda yaci gasar

DUBA WANNAN: Kunar bakin wake a Borno dazu

A cikin miliyan 5.1 din bai hada da kudin talla da kuma masu daukan nauyin shirin daga PayPorte, Heritage bank, MiniMee, Pepsi, Dano milk da sauransu.

Shirin yazo karshe ne a ranar lahadi, Miracle shine jarumin da ya cinye gasar bayan kwanaki 85 da akayi ana shirin tare da wasu mutane 19.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel