Yanzu Yanzu: Kuma dai, yan kunar bakin wake 3 sun sake kai hari garin Borno inda suka kashe kansu

Yanzu Yanzu: Kuma dai, yan kunar bakin wake 3 sun sake kai hari garin Borno inda suka kashe kansu

Jami’an tsaro dakile yunkurin wasu yan kunar bakin wake uku da suka yi kokarin tayar da bam a Bama, dake jihar Borno, hakan ya sanya yan kunar bakin waken suka tayar da kansu inda suka mutu.

Yan sanda sunce yan kunar bakin waken sunyi yunkurin tayar da garin ne da misalin karfe 10:00pm, a ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu, amma jami’an tsaro dake kula da yankin suka gano su sannan suka kalubalance su.

“Yan kunar bakin waken sunyi gaggawar tayar da bam din a jikinsu inda su kadai suka mutu,” jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan Bama, Edet Okon yayi wannan jawabi a ranar Talata.

Yanzu Yanzu: Kuma dai, yan kunar bakin wake 3 sun sake kai hari garin Borno inda suka kashe kansu
Yanzu Yanzu: Kuma dai, yan kunar bakin wake 3 sun sake kai hari garin Borno inda suka kashe kansu

Yan kunar bakin waken sun billo ta yankin Ajilari dake Bama, hanyar da wasu mata yan kunar bakin wake biyu suka bi suka shiga garin a ranar Lahadi day a gabata, sannan suka tayar da bam a yankin wanda yayi sanadiyan mutuwar mutane hudu da raunata wasu takwas.

KU KARANTA KUMA: Sau biyar kawai na kwanta da diyar cikina – Inji wani Uba

A halin da ake ciki, mazauna yankin da sukayi hijira zuwa garin Maiduguri, babban birnin jihar sanadiyan hare-haren Boko Haram a shekarar 2014 sun fara dawowa gidajensu tun a farkon watan Afrilu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng