Labari mai dadin ji: Maganar karin alawus din matasa masu yi wa kasa hidima ta kara tasowa
Shugaban shirin nan na yi wa kasa hidima na gwamnatin tarayyar Najeriya watau National Youth Service Corps (NYSC), mai suna Birgediya Janar Sulaiman Kazaure ya bayyana cewa yadda gwamnatin tarayya ta shirya yin karin mafi karancin albashi ga dukkan ma'aikata shine zai haifar da karin kudaden alawus din matasa masu yi wa kasa hidima.
Birgediya Janar Sulaiman ya bayyana hakan ne a garin Kano ranar litinin din da ta gabata yayin da yake ansa tambayoyi daga 'yan jarida inda ya bayyana cewa tabbas tuni magana ma tayi nisa game da kudurin karin alawus din.
KU KARANTA: Tsohon gwamna ya sha matsa hannun EFCC
Legit.ng ta samu cewa Birgediya Janar Sulaiman ya bayyana cewa tabbas Naira dubu 18 din da ake bayarwa yanzu ko kusa ba su isar matasan wajen yin hidindimun yau da kullum na su.
A wani labarin kuma, Fitaccen dan majalisar dattijan nan dake wakiltar mazabar jihar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya maka gwamnan jihar ta Kaduna a gaban wata babbar kotun jihar inda ya nemi diyyar batancin da yace gwamnan yayi masa har ta Naira biliyan 5.
Mun samu cewa Sanatan dai ya yi wannan rokon ne a matsayin martani ga wata kara da gwamnan ya shigar akan shi a watannin baya inda ya nemi diyyar Naira miliyan 500 daga Sanatan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng