Dandalin Kannywood: Labarin Jaruma Sadiya Adam Idris da baku sani ba

Dandalin Kannywood: Labarin Jaruma Sadiya Adam Idris da baku sani ba

Rahotanni sun kawo cewa jarumar da ta shahara a dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood Sadiya Adam Idris ta kasance daya daga cikin jaruman da suka sha gwagwarmaya da daraktoci da furodusoshi kan ta amshi tayin soyayyarsu saboda kyan diri da kyawawan idanun ta.

Hakan yasa furodusoshi suka yi ta rige-rigen sanya ta a manyan finafinai kuma suka yi ta biyanta manya kudade sama da tsararrakinta don su samu kanta, dalilin da ya sanya cikin dan kankanin lokaci ta yi shahara.

Sai dai wani abinda mutane basu sani ba game da Sadiya Adam shi ne, Sadiya yarinya ce mai rikon addini, domin ma kuwa bincike ya nuna cewa tana daya daga cikin kalilan na mata jarumai da za su iya kawo Baqara zuwa Nasi.

A lokacin da Sadiya ta zo Kano shekaru 4 da suka gabata, ta hadu da wani matasshin dan kasuwa mai suna Sanusi Ahmad, wanda da ne a wajen Ciroman Kantin Kwari kuma mai unguwar Rijiya Biyu a cikin kwaryyar birnin Kano.

Dandalin Kannywood: Labarin Jaruma Sadiya Adam Idris da baku sani ba
Dandalin Kannywood: Labarin Jaruma Sadiya Adam Idris da baku sani ba

Ya kamawa Sadiya gida kuma ya kawata mata shi yadda ta ke bukata, kana kuma ya saya mata tsadaddiyar mota.

Sai dai daukaka da kuma dukiyar da Sadiya ta samu sam bai dadata da kasa ba, hasali ma dai, sai ya kasance jarumar ta ci gaba da bayyana burin da ya kawo ta Kano na ta zama fitacciyar jaruma bayan nan kuma ta samu miji ta yi aure ta zauna a gidanta har abada.

Allah kuwa ya amshi addu’ar Sadiya domin kuwa ya bata duk abinda ta roka a zuwanta Kano. Ita da Sanusi suka shirya angwacewa a ranar 17 ga watan Nuwamban, 2017, amma kash! Sai shirin nasu ya gamu da tasgaru sakamakon son jarumi Ramadan Booth da ya kamata da har ya sanya ta nemi ta fasa auren Sanusi.

Ko da matsin lamba ya yi wa Sadiya yawa na cewa Ramadan fa ba aurenta zai yi ba sai ta saduda ta sake sanya ranar aurenta a matsayin ranar 1 ga watan Afrilu, 2018.

Nan ma dai sai aka sake samun matsala sakamakon kin amincewa da iyayen Sanusi suka yi na ya auri ‘Yar Fim’, kamar dai yadda majiyarmu ta bayyana mana.

Daga bangaren iyayen Sadiya ma dai an samu irin waccan matsalar sakamakon wai su sun fi amincewa da Sadiya ta koma gida Maiduguri ta auri dan uwanta.

Hakan ya sanya dole Sadiya ta tattara ya-nata-ya nata ta koma Maiduguri kuma ta daina ko yin waya da abokan aikinta na Kannywood.

Can daga baya kuma sai jita-jita ta ci gaba da yaduwa a industiri na cewa fa batun auren Sadiya a ranar 1 ga watan Afrilu, 2018 na nan ba a fasa ba sakamakon ganin kawayenta na kusa suna ‘yan shirye-shirye.

KU KARANTA KUMA: Sau biyar kawai na kwanta da diyar cikina – Inji wani Uba

Bayan an kai Sadiya dakinta ne sai ta rubuta a shafinta na Instagram cewa tana bukatar ‘yan uwa da abokan arziki da su taya ta da addu’ar samun zaman lafiya a gidan mijinta.

Sai dai wata majiya ta ce wasu daraktoci da furodusoshin Kannywood basa yi wa Sadiya fatan ta zauna a gidan mijin nata, saboda basu koshi da samun riba daga irin rawar da jarumar ke takawa a finafinai ba, a cewar majiyar.

Idan bazaku manta ba a baya Legit.ng ta kawo maku cewa an daura auren a garin Kano a masallacin Umar Bin Khattab da ke shataletalen Dangi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel