Wani ma’aikacin NAF da aka kora yace sun shiga gonar Magu ne don su samo kudi

Wani ma’aikacin NAF da aka kora yace sun shiga gonar Magu ne don su samo kudi

- Hukumar ‘Yan Sanda ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kai hari a gonar shugaban hukumar kula da hakkin tattalin arzikin Najeriya mai rukon kwarya, Ibrahim Magu

- Harin wanda mutanen suka kai a gidan gonar yayi sanadiyar ran jami’in ‘Yan Sanda mai suna Sajan Haruna Sarki

- Wanda ake zargin sun hada da tsohon ma’aikacin hukumar Sojin Sama ta Najeriya wanda ta kora, Vincent Michael

Hukumar ‘Yan Sanda ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kai hari a gonar shugaban hukumar kula da hakkin tattalin arzikin Najeriya mai rukon kwarya, Ibrahim Magu.

Harin wanda mutanen suka kai a gidan gonar yayi sanadiyar ran jami’in ‘Yan Sanda mai suna Sajan Haruna Sarki, wanda yake gadi a gidan gonar.

Wanda ake zargin sun hada da tsohon ma’aikacin hukumar Sojin Sama ta Najeriya wanda ta kora, Vincent Michael, mai lamba NAF12/26972L/CPL, sai Inalegwu Omikpa da kuma Francis Ochife.

Michael ya bayyanawa ‘yan jarida a ranar Litinin a birnin tarayya cewa sun kai harin ne sakamakon labari da suka samu cewa Ibrahim Magu ya ajiye makudan kudi a gidan gonar nasa. Sannan yace Omikpa ya kashe dan Sandan dake gadi a gonar.

Wani ma’aikacin NAF da aka kora yace sun shiga gonar Magu ne don su samo kudi
Wani ma’aikacin NAF da aka kora yace sun shiga gonar Magu ne don su samo kudi

Mataimakin mai magana da yawun hukumar Sojin SP Aremu Adeniran yace sun bayar da Michael zuwa ga hukumar ‘Yan Sanda bayan korarsa da sukayi sakamakon hannun da yake dashi a harin da aka kai, sannan kuma akwai wasu jami’an Sojin biyu wadanda suma suna da hannu a ciki, suna fuskantar horo sannan za’a mikasu ga ‘Yan Sanda idan an sallamesu.

KU KARANTA KUMA: Rahma Sadau ta caccaki Atiku Abubakar

A halin da ake ciki, a makon da ta gabata ne Legit.ng ta rahoto cewa hukumar yan sandan Najeriya ta kara ma mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu matsayi zuwa kwamishinan yan sanda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel