Mage da bera: Sanata Shehu Sani ya maka Gwamna El-Rufai kotu, ya nemi diyyar Naira biliyan 5
Fitaccen dan majalisar dattijan nan dake wakiltar mazabar jihar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya maka gwamnan jihar ta Kaduna a gaban wata babbar kotun jihar inda ya nemi diyyar batancin da yace gwamnan yayi masa har ta Naira biliyan 5.
Mun samu cewa Sanatan dai ya yi wannan rokon ne a matsayin martani ga wata kara da gwamnan ya shigar akan shi a watannin baya inda ya nemi diyyar Naira miliyan 500 daga Sanatan.
KU KARANTA: An yi yunkurin hambarar da daular Saudiyya
Legit.ng ta samu haka zalika cewa ma Sanatan ya kuma roki kotun da ta sakawa bakin gwamnan linzami musamman ma wajen yin batanci a gare shi da sauran mukarraban sa a gidajen yada labaran jihar dama dukkan kasar baki daya.
A wani labarin kuma, Labarin da muke samu sun tabbatar mana da cewa hukumar nan da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gwamnatin tarayya watau Economic and Financial Crimes Commission, EFCC ta tutse tsohon gwamnan jihar Filato har na tsawon awayi bakwai.
Mun samu haka zalika cewa hukumar ta EFCC ta matsi Sanatan da yanzu haka yake wakiltar mazabar jihar Filato ta Arewa ne bisa zargin almundahana na zunzurun Naira biliyan biyu na kudaden al'umma.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng