Umarni daga Koto: Kada ku sake buga sunan shugaban PDP cikin sunayen barayi

Umarni daga Koto: Kada ku sake buga sunan shugaban PDP cikin sunayen barayi

- Shugaban PDP yayi galaba kan Lai Muhammed

- Kotu ta bayar da umarnin kada a sake buga sunansa cikin barayin gwamnati

- Shi kuma yana neman Kotun ta sanya a biya shi makudan kudade a matsayin diyyar bata sunansa

Wata babbar Kotu dake zamanta a birnin fatakwal ta dakatar da sake wallafa sunan shugaban jam’iyyara PDP na kasa Uche Secondus, cikin jerin sunayen barayin gwamnati da ake zargi.

Umarni daga Koto: Kada ku sake buga sunan shugaban PDP cikin sunayen barayi
Uche Secondus shugaban PDP na kasa

Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Iyayi Laminikara, ya bukaci mai karar da ya tabbatar ya aike da sakon sabon hukuncin da kotun ta yanke ga wanda ake karar.

Tsagen wadanda ake karar basu samu damar halartar zaman kotun ba da aka fara yau, tun bayan da shugaban jam’iyyar ta PDP Uche Secondus, ya shigar da karar Ministan tun ranar shida ga wata Afrilu.

Da farko dai shugaban PDP ya bukaci Ministan da ya cire sunansa sannan ya rubuta wasikar bashi hakuri da neman afuwarsa cikin awa 48, ko kuma ya kais hi kara.

kafin daga bisani ya shigar da karar yana neman a biya shi zunzurutun kudin da yakai biliyan daya da rabi (N1.5b) a wani jawabi da mataimakin shugaban PDP a bangaren yada labarai Ike Abonyi, ya fada.

KU KARANTA: Atiku ma ya taba cewa ‘yan arewa malalata - Kungiyar kare hakkin musulmai ta kare Buhari

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammed, ya fitar da jadawalin sunayen wadanda ake zargin a ranar 19 ga watan Fabarairus sunyi waka ci waka tashi da kudin makamai daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki, inda Ministan ya bayyana shima shugaban PDP ya karbi har Naira miliyan 200.

Umarni daga Koto: Kada ku sake buga sunan shugaban PDP cikin sunayen barayi
Umarni daga Koto: Kada ku sake buga sunan shugaban PDP cikin sunayen barayi

A bisa bijirewa sharadin rubuta wasikar ba shi hakuri da kuma cire sunansa ne, ya sanya yanzu Secondus ya shigar da kara don bi masa kadinsa.

A cewar takardar karar mai lamba “no/PHC/1013/2018, ya roki kotun da ta bi masa hakkkinsa yi masa kazafi sannan kuma da umartar Ministan ya biya shi kudi N1.5 a matsayin kudin bata suna da yayi masa sakamakon zubar masa da mutunci da kima da aka yi a dalilin wallafa sunan nasa.”

Sai dai a zaman na yau, lauyoyin wanda yake kara ne kawai suka samu damar halarta karkashin jagorancin Emeka Etiaba, don fara shari’ar. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel