Ke Duniya: ‘Yan uwa biyu sun taru sun kashe dan uwansu sannan suka tsige kanshi kamar Kashu

Ke Duniya: ‘Yan uwa biyu sun taru sun kashe dan uwansu sannan suka tsige kanshi kamar Kashu

Wasu yan uwa su biyu masu suna Akaninyene da kuma Ime Enyeokpon, sun yi hadin kwanji wajen kashe dan uwansu mai suna Friday Enyeokpon, wai kawai don suna zargin yayi musu asiri.

Yanzu haka dai rundunar yan sanda ta jihar Akwa Ibom tayi ram da su.

Marigayin wanda shi ne da na biyu a gidansu, an ce ya tafi cikin daji ne duba tarkon kama namun dajin da ya dana ne, yan uwan suka kashe shi.

Da yake Magana kan faruwar lamarin kwamishinan yan sanda na jihar Mr. Adeyemi Ogunjemilusi, da yayi magana ta hannun kakakin rundunar DSP Odiko MacDon ya ce, bayan an gudanar da bincike,wadanda ake zargin sun bayyana yadda su kai fakon dan uwan nasu a daji sannan suka far masa suka rika dukansa har sai da ya mutu sannan suka tsige kansa suka binne suka kuma yasar da gangar jikinsa a dajin.

KU KARANTA: Maganin sanyi, rage kiba da sauran irin amfanin da goro yake yi ga mutum

yanzu haka dai sun amsa laifin nasu, amma sai dai kun kafe akan cewa lallai-lallai asiri yayi musu domin rayuwar su ta balbalce.

Kakakin yan sanda ya kuma ce, "sun tono kan mamacin har ma an kai shi sashin ajiyar gawarwaki a asibiti. sannan kuma sun gano adduna har biyu da suka yi amfani da su wajen kashe mamaci". Kuma zasu cigaba da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng