Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur (hotuna)

Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur (hotuna)

- Sojojin 81 Division sun sake kama wasu mutane 23 da ake zargin ‘yan kungira asiri ne a unguwar Ikorodu dake jihar Legas

- Sojojin sun samu labarin cewa suna horar da sababbin ‘yan kungiyar a kalla mutane 50 daga Eiye, suna shirye shiryen fashin da makami da kuma garkuwa da mutane

- Sojojin sunyi nasarar kama 23 cikin mutanen bayan gwagwarmaya da musayar wuta da suka sha tsakanin Sojojin bataliya ta 174 na unguwar ta Ikorodu da kuma ‘yan kungiyar ta asiri

Sojojin 81 Division sun sake kama wasu mutane 23 da ake zargin ‘yan kungira asiri ne a unguwar Ikorodu dake jihar Legas. Sojojin sun samu labarin cewa suna horar da sababbin ‘yan kungiyar a kalla mutane 50 daga Eiye, suna shirye shiryen fashin da makami da kuma garkuwa da mutane.

Sojojin sunyi nasarar kama 23 cikin mutanen bayan gwagwarmaya da musayar wuta da suka sha tsakanin Sojojin bataliya ta 174 na unguwar ta Ikorodu da kuma ‘yan kungiyar ta asiri. Biyu daga ciki sun samu rauni sanadiyyar habin bindiga.

Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur
Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur

Daya daga cikin sababbin daukar kuma ya rasa ransa sakamakon jinin da ya zubar a wurin gudanar da al’adunsu na kungiyar. Sai daya daga cikin jarumar Sojojin ya samu rauni a kafarsa ta hagu sakamakon harbinsa da akayi a wurin gwagwarmayar.

KU KARANTA KUMA: An kama wani mutumi bisa zargin yiwa yar shekara 13 fyade

Da Sojan wanda ya samu rauni a kafa da kuma sauran ‘yan kungiyar biyu da suka samu rauni sun asibitin Bataliyar sojan ta Medical Reception Station ana kulawa dasu.

Abubuwan da aka samu a hannun ‘yan kungiyar sun hada da bindigar kugu ta hausa 1, sai akwatin harsasai 5, sai adduna 5, wukaken kugu na sojoji 4, sai wukaken kicin 2, sai tsitaka 3, saiwayoyin salula 5, sai roba dauke da tabar wiwi, sannan sai katin ATM 2, sai katin tantance mutane 8, sai kananan hotuna 8, sai pakitin kororon roba, sai zobuna da kuma kayayyakin tsubbu.

Ga karin hotuna a kasa:

Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur
Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur

Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur
Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur

Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur
Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng