Iyayen yan matan Chibok sun mutu a wata mummunan hadarin Mota
Wasu iyayen yan matan Chibok sun gamu da mummunan hadari a ranar Lahadi, 22 ga watan Afrilu yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ganin yayan nasu dake karatu a jami’ar ABTI dake garin Yola na jihar Adamawa.
Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito a shekarar data gabata ne gwamnatin tarayya ta amso wasu yan mata daga cikin yan matan da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta sace tun a shekarar 2014, inda bayan sakin nasu ne gwamnati ta dauki nauyin karatunsu a jami’ar Amurka dake jihar Adamawa.
KU KARANTA: Mutane 7 ne suka mutu yayinda 12 suka jikkata a harin da aka kai masallacin Bama
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a sakamakon wannan mummunan hari, guda cikin iyayen ya rigamu gidan gaskiya, yayin da guda goma sha bakwai suka jikkata, inda 5 daga cikinsu suka samu karaya a hannaye da kafafuwa.
“Da sanyin safiya muka fita daga garin Chibok a cikin maotocin Bas guda bakwai, muka nufi Yola, zuwa jami’ar Amurka dake Yola don ganin yaranmu dake karatu a can, muna cikin tafiya ne sai kan motar ta kufce ma guda cikin direbobin.
“Daga nan sai motar ta bugi wata motar ta daban, sakamakon hakan mutum guda ya rasa ransa, 17 sun jikka,a yayin da mutane 5 suka karairaye.” Inji Yana Galang, wata yar kungiyar ceto yan matan Chibok.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng