Mutane da dama sun jikkata yayinda Yarbawa da Hausawa suka kara a Ondo
- An samu rashin kwanciyar hankali a garin Ondo a ranar Lahadi, sakamakon Yarabawa sun shiga rikici tsakaninsu da wasu hausawa mazauna garin wanda yayi sanadiyyar mutane da dama suka samu raunuka
- Rikicin ya biyo bayan wasu mabiyan al’adarsu na was an gargajiya dake Akure wadand suka shiga unguwar Sabo inda yawanci hausawa ne mazaunan wurin
- Mabiyan kungiyar al’adun sun ratsa ta unguwar ne, inda suka hana hausawan gudanar da kasuwancinsu wanda hakan ya kawo rikicin
An samu rashin kwanciyar hankali a garin Ondo a ranar Lahadi, sakamakon Yarabawa sun shiga rikici tsakaninsu da wasu hausawa mazauna garin wanda yayi sanadiyyar mutane da dama suka samu raunuka.
Majiya ta bayyana cewa “rikicin ya biyo bayan wasu mabiyan al’adarsu na was an gargajiya dake Akure wadand suka shiga yankin tsohon gareji, inda hausawa ke gudanar da kasuwancinsu mazaunan wurin.
Mabiyan kungiyar al’adun sun ratsa ta unguwar ne, inda suka hana hausawan gudanar da kasuwancinsu wanda hakan ya kawo rikicin. An samu cushewa hanya a Oba Adesina Road na tsawon awoyi wanda har ya janyo aka kona wasu mashina sai kuma gidajen mutane da aka taba.
Mista Femi Joseph, jami’in ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a ya tabbatar da cewa an tura ‘Yan Sanda da kuma na Soja na 32 Artillery Brigade, wadanda suka kawo kwanciyar hankali a yankin suka tsayar da rikicin, ya kuma kara da cewa sun fara gudanar da bincike game da lamarin.
KU KARANTA KUMA: Dakarun sojoji sun kama manyan yan fashi a jihar Kogi
Babban Sakataren Deji na garin Akure, Oba Aladelusi Aladetoyinbo, Mista Micheal Adeyeye, yace fadar garin ma tana gudanar da nata binciken game da lamarin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng