Yanzu Yanzu: An kama Sanata Melaye a filin jirgin sama
A yanzu haka an kama Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi West a filin jirgin sama na Abuja.
A cewar wani rubutu da Sanatan ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu, sanatan yace an kama shi ne a hanyarsa ta zuwa Morocco domin ziyarar aiki.
Melaye ya rubuta: “Yanzun nan aka kama ni a filin jirgin sama na Abuja wato Nnamdi Azikiwe airport a hanyata na zuwa Morocco domin gudanar da wani aiki da yardar gwamnatin tarayya.”
KU KARANTA KUMA: Satar sandar girma ta majalisa rahama ce a lullube - Sanata
Ku tuna cewa a ranar Laraba, 28 ga watan Maris, yan sanda sun sanar da neman Dino Milaye ruwa na jallo. An kaddamar da neman dan majalisar ne tare da Mohammed Audu, dan tsohon gwamnan jihar Kogi, Abubakar Audu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng