Tamu ta samu: Yadda 'yar Najeriya mai shekaru 16 ta kwashi 'yan kallo a jami'ar kasar Amurka
Wata 'yar shekara 16 a duniya kacal 'yar asalin kasar Najeriya amma wadda ke zaune a kasar tarayyar Amurka mai suna Oluwatofunmi Oteju ta kwashi 'yan kallo bayan da ta lashe kyautar 'shugaba' ta shekara a jami'ar Augsburg.
Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, Oluwatofunmi an karramata ne a ranar Lahadin da ta gabata domin kara mata karfin gwuiwa akan ficen da tayi a wani darasi kan shugabanci.
KU KARANTA: Gwamnoni 5 da ake sa ran za su zarce a 2019
Legit.ng ta samu cewa ba tun yau ne ba dai wasu 'yan Najeriya din ke yin fice a fannoni daban daban na rayuwa a ciki da kuma wajen kasar nan.
A wani labarin kuma, Gwamnatin kasar hadaddiyar daular Ingila ta yi alkawarin baiwa kasar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari kayayyakin zamani na yakar 'yan ta'addan Boko Haram da suka kai na darajar Fam miliyan daya.
Babban ministan kasar Ingila din ne dai na fannin tsoji Mista Mark Lancaster ya sanar da hakan yayin tattaunawar sa da takwaran sa na tsaron Najeriya Mansur Dan-Ali a birnin Landan din.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng