Babbar magana: An yi yunkurin hambarar da masarautar daular Saudiyya

Babbar magana: An yi yunkurin hambarar da masarautar daular Saudiyya

Kamar dai yadda muka samu daga wasu majiyoyin mu, kafafan yada labaran kasar Amurka sun rawaito cewa wasu sun yi yunkurin yin juyin mulkin a daular kasar Saudiyya a karshen makon nan da muke ciki.

Babbar magana: An yi yunkurin hambarar da masarautar daular Saudiyya
Babbar magana: An yi yunkurin hambarar da masarautar daular Saudiyya

KU KARANTA: Makusantan Buhari 5 da ke zama gwamnoni a 2019

Majiyar mu ma dai ta ayyana cewa a yayin da aka ji karar fashewar wasu ababe masu karar gaske da kuma harbin bindigogi a kusa da fadar sarkin daular ta Saudiyyya, wasu daga cikin kafafan yada labaran kasar Amurka sun yi zargin cewa wasu daga cikin kwamandan sojojin kasan Saudiyya karkashin jagorancin Alukas Nepils tare da wasu gungun sojoji sun yi yunkurin hambarar da mulkin sarki Salman.

Legit.ng ta samu cewa sai dai, wasu daga majiyoyin na mu kuma sun rawaito ne cewa rikicin cikin gida ne yayin da magoyan bayan yarima Talal bin Walid ne ke yunkurin yin juyin mulkin.

Haka ma dai mun samu tabbacin cewa jiragen yaki da masu saukar angulu sun yi ta shawagi a sararin samaniyar Riyadh babban birnin daular.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng