Tirka-Tirka: Hukumar EFCC ta taso matar Saraki gaba bisa zargin badakalar ma'aikatan bogi

Tirka-Tirka: Hukumar EFCC ta taso matar Saraki gaba bisa zargin badakalar ma'aikatan bogi

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta bayyana cewa zata fara binciken da ya kamata game da takardar korafin da suka samu na zargin badakalar ma'aikatan bogi da hadimi da kuma matar shugaban majalisar dattijai ke ciki.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Mista Wilson Uwajaren shine ya sanarwa da wakilin majiyar mu hakan a wata tattaunawar da sukayi ta wayar tarho da yake neman karin bayani.

Tirka-Tirka: Hukumar EFCC ta taso matar Saraki gaba bisa zargin badakalar ma'aikatan bogi
Tirka-Tirka: Hukumar EFCC ta taso matar Saraki gaba bisa zargin badakalar ma'aikatan bogi

KU KARANTA: Zaben 2019: INEC ba za ta yi adalci ba - PDP

Legit.ng ta samu dai cewa wani ne ya rubutawa hukumar ta EFCC takardar korafin zargin a watannin baya.

A wani labarin kuma, Akalla mutane uku ne ciki hadda babban malamin addinin kirista suka rasa ransu a wajen taron tattaunawa na jam'iyyar APC mai mulki a jihar Benue dake a shiyyar Arewa ta tsakiya, ranar Juma'ar da ta gabata a garin Otukpo.

Wakilin majiyar mu dai ya bayyana mana cewa jim kadan bayan fara taron ne sai fada ya barke a tsakanin mabiya bangarori biyu da basu ga maciji da juna na shugaban jam'iyyar na jiha da kuma wani dan majalisar tarayya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng