Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna

Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna

- Tsugunno bai kare ba a rigimar Gwamnan Kaduna da Malaman da ya kora

- Ma'aikatan sun ce su kawai a biya su kudadensu a kyale su a daina damunsu yayinda suka bijirewa shirin koyar dasu sana'o'i

Yanzu haka dai daruruwan Malaman da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya kora sun kekasa kasa sunki yarda da tsarin koya musu san’o’i a ranar Juma’a da gwamnatin jihar zata yi a garin Zaria.

Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna
Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna

Da suke yiwa wadanda aka turo domin basu horo kan sana’o’in jawabi, fusasattun korarrun Ma’aikatan sunce su kawai a biya su kudadensu na sallama daga aiki basu damu da wata sana’ar da ake shirin koya musu ba.

An dai shirya horaswar ne a kwalejin ilimi ta Al’huda-huda dake garin Zaria, ga Malaman da suka fito daga kananan hukumomin Zaria da Sabongari da Soba da kuma Giwa bayan yi musu ritayar, karkashin kulawar babban sakataren ma’aikatar ilimi ta jihar.

Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna
Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna

Anyi wa wasu daga cikin korarrun Ma’aikatan ritayar dole ne bayan faduwa jarrabawar cancanta da gwamnatin jihar ta shirya a watannin baya.

A cewar Ma’aikatan, sunzo wurin da tunanin za’a biya su kudadensu, bayan anyi duk mai yiwuwa ta gagara domin shigar da su dakin bayar da horon.

Malam Adamu Lawal, guda ne daga cikin tsofaffin Malaman kuma ya shaidawa manema labarai cewa, “Sunyi mutukar mamaki da har yanzu ba’a biya su hakkin nasu ba, bayan kuma gwamnatin jihar tayi ta nanata cewa zata biya su, tunda muna cikin aikinmu haka kawai kwatsam aka kore mu amma har yanzu shiru kake ji ba’a biya mu kadadenmu ba”.

KU KARANTA: Kaico: Karanta yadda Mata suke illata jikinsu da sunan ado don burge Maza

“Mu da suka kira mu nan, munyi zaton ko zasu fada mana yadda zamu bi domin karbar kudaden namu. Amma sai suke fada mana cewa mu zauna zasu horas da mu sana’a sannan su bamu bashi. Baza mu karbi wani bashi ba, abinda kawai muke so shi ne kudinmu”. Malam Adamu ya bayyana cikin fushi.

Shi ma wani da aka yiwa ritayar mai suna Yusuf Yakubu daga karamar hukumar Sobo cewa yayi, “Horaswar bata da wani muhimmanci a gare su, da suka fara bayar da fam din nayi zaton na biyanmu ne, har na karba sai naga ashe horo zasu bamu sannan da bashin kudi, wanda duk banson su”

Maryam Muhammad wacce ita ma korarriyar Malama ce daga karamar hukumar Zaria ta shaidawa majiyarmu cewa, “Murnarta ta koma ciki a sakamakon abinda ta tarar, don tazo wurin ne tun karfe shida na safe a dalilin labarin da ta samu na mayar da su aiki da aka ce gwamnatin jihar za tayi”.

Yawan ma’aikatan dai sun bayyana cewa yanzu haka ma ana binsu bashin mai tarin yawa, don haka baza su yarda su karawa kansu wani bashin ba.

Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna
Kaka-kara-kaka: Rigima an shiga turmi na biyu tsakanin Malaman da El-Rufa’I ya kora a Kaduna

“Abin kunya ne ace har yanzu gwamnati ta gaza biyanmu kudaden na mu, kamata yayi a fara biyanmu hakkinmu sannan sai a bullo da shirin koyan sa’a da bayar da bashin” a cewar wata Malama Ruya Mathew da ta fito daga karamar hukumar Zaria.

Shi ma wani Malami da akaiwa ritayar dolen mai suna Sarki Kofar-Doka ya bayyana cewa, tunda sun yarda da batun korar tasu da akayi kamata yayi kawai gwamnatin ta biya su hakin nasu, tunda dai in ba kira babu abinda zaici gawayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel