Kaico: Karanta yadda Mata suke illata jikinsu da sunan ado don burge Maza
- Garin neman gira za'a rasa ido
- Zamani na canzawa, sutura na canzawa haka kwalliya na canzawa, karanta yadda Mata ke azabtar da kansu da sunan gayu
Zamanin yanzu Mata gaba daya hankalinsu ya karkata ne ga burge Maza, komai za suyi burinsu su ja hankali a kale su don ace sun fi sauran mata.
Sukan yi gyaran gashi ko kara shi idan basu da shi, su kara farce da gira ko kuma su sha maganin karin mama da mazaune duk don su burge Maza.
To amma sai dai wani abu da basu gane ba shi ne, wasu lokutan kwalliyar da suke yi don burge mazan, kan cutar da lafiyarsu ta ciki ko ta waje.
Legit.ng tayi duba izuwa kwalliyar da wasu matan kanyi don burge maza da irin illar da kwalliyar take yiwa jikinsu watakila batare da sun sani ba.
Wani shahararren mai daukar hoto mai suna Justin Bartels, ya daukar gabarar gudanar da tunanin yadda Mata ke takura kansu ta hanyar sanyawa ko daura kayan da ya matse su sosai don su jawo hankalin Maza garesu.
Bartels yace ya fara tunanin bincikar dabi’ar Matan ne tun lokacin yana kwaleji, lokacin yana tsaka da soyayya da yan Mata daban-daban.
Yace, “Wato abin na bani mamaki ganin yadda Matan kan iya sanya kayan da su kansu basa jin dadinsa ko ya matse su ko kuma yayi musu kadan kawai don burge Maza da niyyar ajinsu ya daga”. A cewar Bartels.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe wani gawurtacen 'dan ta'ada a jihar Akwa Ibom
Yadda suke matse kugunsu don ace suna da babban kugu da kuma shatin illar da yayi.
Bartels ya kuma ce, "Ina fata idan masu irin wannan kasassabar da sunan burge Maza sau farga su gane cewa, akwai hanyoyi da yawa na jan hankali da burge maza ba lallai sai sun cutar da kansu ba".
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng