Wani 'Dan Kasuwa ya caccaki Keyamo kan batun amincewa da yiwa Shugaba Buhari hidima
A ranar Juma'ar makon da ya gabata wani 'Dan kasuwa Bobby Uzochukwu, ya cacccaki babban lauya Mista Festus Keyamo a farfajiyar babbar kotun tarayya dake birnin Awka a jihar Anambra, inda ya kalubalance shi dangane amincewar sa ta kasancewa Kakakin kungiyar yakin neman zabe ta shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Uzochukwu dai ya tuhumi Keyamo dan sayar da kansa sakamakon amincewar sa ta yiwa kungiyar kamfe ta kujerar shugaba Buhari hidima dangane da zaben 2019 mai gabatowa.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, a kwanan-kwanan nan ne aka yiwa babban lauyan tayin wannan mukami a wata rubutacciyar wasika da sanadin jam'iyyar APC ta kasa kuma ya amince ba tare da wata tangarda ba.
Legit.ng ta fahimci cewa, Keyamo ya sha suka ne a yayin da yake ganawa da manema labarai kasancewar sa lauya mai kare wani mutum dangane da kashe-kashen da ya afku na ranar 6 ga watan Agusta a Cocin St. Philips dake garin Ozubulu a jihar ta Anambra.
KARANTA KUMA: Ku tabbata kun zabi 'Yan takara Nagari - Shehi Dahiru Bauchi ga Al'ummar Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa, Uzochukwu ya kirayi Keyamo da sunaye irin na cin mutunci, muzantawa da kuma zagi irin na kare dangi.
Wannan lamari ya sanya Keyamo ya katse ganawar sa da 'yan jarida inda ya shige motar sa kuma ya kama gaban sa.
Cikin banbami Uzochukwu ya ci gaba da cewa, ya yi mamakin yadda amininsa Keyamo zai ci amanar su sakamakon amincewa wajen yiwa shugaba Buhari hidima duk da ya juya bayan sa ga al'ummar kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng