Najeriya ta wadata da matasa masu kwazo da kokari - PDP

Najeriya ta wadata da matasa masu kwazo da kokari - PDP

- Jam’iyyar PDP ta amince da cewa Najeriya har yanzu bata gano muhimmanci da basirar matasa, mutane ne masu kokari da hazaka ba

- Shugaba Buhari a cikin wani bidiyo da aka fitar yace dayawan matasan Najeriya da basu wuce shekaru 30 ba basu da ilimi, kuma suna jira komai sai anyi masu

Sakataren jam’iyyar ta PDP ya bayyana cewa kalaman da shugaba Buhari yayi game da matsan Najeriya ya raunata masu tinaninsu ga idon duniya data sansu da kwazo

Jam’iyyar PDP ta amince da cewa Najeriya har yanzu bata gano muhimmanci da basirar matasa ba, mutane ne masu kokari da hazaka.

Sakataren jawabai na jam’iyyar PDP Mr Kola Ologbondiyan ya bayyana haka a ranar Alhamis bayan kwana daya da kamala taron kungiyar zartarwa ta jam’iyyar, a birnin tarayya.

Shugaba Buhari a cikin wani bidiyo da aka fitar yace dayawan matasan Najeriya da basu wuce shekaru 30 ba basu da ilimi, kuma suna jira komai sai anyi masu kawai saboda suna ganin cewa Najeriya nada arzikin mai.

Najeriya ta wadata da matasa masu kwazo da kokari - PDP
Najeriya ta wadata da matasa masu kwazo da kokari - PDP

Sakataren jam’iyyar ta PDP ya bayyana cewa kalaman da shugaba Buhari yayi, game da matsan Najeriya ya raunata masu tinaninsu ga idon duniya data sansu da jajircewa da kwazo. Wanda dayawan mutanen Najeriya basuji dadin wadannan kalamai na shugaba Buhari ba.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Najeriya tayi jawabi game da kisan jami’inta da mutanen Binuwai sukayi

Saboda haka jam’iyyar ta PDP tayi kira ga matasan Najeriya dasu hada kai da ita, don ganin sun kawar da wannan gwamnatin ta APC a zaben 2019 mai zuwa. Saboda APC bata nuna wata damuwa ba game da cigaban matan Najeriya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng