Sakamakon fashi da makami da akayi a garin Offa an canzawa kwamishinan ‘Yan Sandan jihar wajen aiki
- Shugaban hukumar ‘Yan Sanda Ibrahim Idris ya canza kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar ta Kwara Alhaji Lawan Ado cikin gaggawa
- Shugaban hukumar Ibrahim Kpotun Idris tare da Gwamnoni da Sarakuna da sauran baki na taron da aka gudanar a jihar Kaduna na masu ruwa da tsaki a Arewa game da tsaro, ya bayyana Aminu Pai Saleh a matsayin sabon kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar
- Shugaban hukumar yace duk da anyi nasarar kama wasu wadanda ake zargi da hannu a cikin fashin da akayi akwai Mr Kayode Opadokun wanda da ne ga tsohon dan jarida na farko Chief Ayo Opadokun
Shugaban hukumar ‘Yan Sanda Ibrahim Idris ya canza kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar ta Kwara Alhaji Lawan Ado cikin gaggawa, ya mayar dashi makarantar horar da ‘Yan Sanda dake jihar Kaduna.
Shugaban hukumar Ibrahim Kpotun Idris tare da Gwamnoni da Sarakuna da sauran baki na taron da aka gudanar a jihar Kaduna na masu ruwa da tsaki a Arewa game da tsaro, ya bayyana Aminu Pai Saleh a matsayin sabon kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar.
Shugaban hukumar yace duk da anyi nasarar kama wasu wadanda ake zargi da hannu a cikin fashin da akayi akwai Mr Kayode Opadokun wanda da ne ga tsohon dan Jarida na farko Chief Ayo Opadokun, a cikin firaministan dake zargin.
Kafin mayar da Saleh jihar Kwara a matsayin kwamishinan ‘Yan Sanda ya kasance yana shugabancin makaratar horar da ‘Yan Sanda ta Kaduna, inda shugaban hukumar ya umurce shi da ya fara aiki daga ranar Juma’a.
KU KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Najeriya tayi jawabi game da kisan jami’inta da mutanen Binuwai sukayi
Majiyoyi daban daban sun bayar da rahotanni da dama inda wasu suka bayyana cewa lokacin cinza shi ne yayi shiyasa aka canza shi ba wai saboda fashin da akayi bane yasa aka canza shi ba, inda wasu kuma suka nuna cewa an canzashi ne sakamakon fashin da akayi wanda yayi sandiyyar mutuwar jami’an ‘Yan Sanda 9.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng