Hukumar Sojin Najeriya tayi jawabi game da kisan jami’inta da mutanen Binuwai sukayi

Hukumar Sojin Najeriya tayi jawabi game da kisan jami’inta da mutanen Binuwai sukayi

- Hukumar Sojin Najeriya ta darkaki wani kauye a jihar Binuwai sakamakon mutanen garin sun kashe wani jami’in Sojin

- Sojin sun gona gidaje da kuma kayayyakin mutanen kauyen lokacin da suka shiga kauyen daukar fansa

- Sojin wadanda aka tura suyi bincike a gurin da lamarin ya auku sun kama wasu daga cikin mutanen garin wadanda ake zargi

Hukumar Sojin Najeriya tayi bayani game da yanda ta darkaki wani kauye a jihar Binuwai sakamakon mutanen garin sun kashe wani jami’in Sojin.

Sojin sun kona gidaje da kuma kayayyakin mutanen kauyen lokacin da suka shiga kauyen daukar fansa.

Legit.ng ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan kisan wani jami’in Soja da mutanen garin sukayi kuma suka rufeshi a wani rami mara zurfi a kauyen Naka dake karamar hukumar Gwer a jihar da misalin karfe 11:00 na dare.

Premium Times ta ruwaito cewa Sojin wadanda aka tura suyi bincike a gurin da lamarin ya auku sun kama wasu daga cikin mutanen garin wadanda ake zargi.

Hukumar Sojin Najeriya tayi jawabi game da kisan jami’inta da mutanen Binuwai sukayi
Hukumar Sojin Najeriya tayi jawabi game da kisan jami’inta da mutanen Binuwai sukayi

Francis Ayagah wanda shine Ciyaman na karamar hukumar, ya amsa cewa da gaske an kashe jami’in Sojin a cikin garin a ranar Laraba 18 ga watan Afirilu, amma dai ya bayyanawa shugaban jami’an Sojin wadanda ke kusa da garin nasu.

Anyi ikirarin cewa mazauna yankin sun yi kuskuren daukar sojan a matsayin dan ta’adda lokacin da suka gansa kusa da wani gona sannan suka far masa har lahira.

Olabisi Ayeni wanda shine mai magana da yawun hukumar Sojin ta 707 Special Forces Brigade dake Makurdi, ya bayyana cewa Sojan wanda aka kashe sunansa Danlami Gambo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng