Wata sabuwa: Kotu ta hana 'yan sanda da jami'an SSS su kama Sanata Ovie Omo-Agege

Wata sabuwa: Kotu ta hana 'yan sanda da jami'an SSS su kama Sanata Ovie Omo-Agege

Wata babbar kotu dake a unguwar Maitama a garin Abuja, babban birnin tarayya ta bayar da umurmi ga jami'an tsaron Najeriya da suka hada da 'yan sanda da kuma jami'an tsaron farin kaya watau SSS da kar su kuskura su kama Satana Ovie Omo-Agege daga jihar Delta.

Wannan dai kamar yadda muka samu ya biyo bayan bukatar Lauyan Sanatan mai suna Aliyu Umar ya roki kotun a cikin karar da ya shigar a gaban ta .

Wata sabuwa: Kotu ta hana 'yan sanda da jami'an SSS su kama Sanata Ovie Omo-Agege
Wata sabuwa: Kotu ta hana 'yan sanda da jami'an SSS su kama Sanata Ovie Omo-Agege

KU KARANTA: Masu takarar shugabancin kasar Najeriya a 2019 sun kara yawa

Legit.ng dai ta samu cewa Sanatan na fuskantar barazanar kamu ne daga jami'an tsaron bayan an zarge shi da jagorantar tawagar katti da suka shiga majalisar dattijan suka kuma sace sandar girma a farkon satin nan.

A wani labarin kuma, Shugaban hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance, mallakin gwamnatin tarayya mai suna Ibrahim Magu ya bayyana cewa shi da kansa ya shawarci a kori manyan daraktocin hukumar nan ta NEMA da aka samu da laifin badakalar kudi.

A cewar sa, tun a watan Disembar bara ne dai hukumar ta sa ta samu wata takardar korafi akan wadanda ake zargin inda bayan sun bincika kuma suka tabbatar da aikata laifukan na su sannan kuma suka shawarci a dakatar da su har sai an kammala bincike.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng