Yanzu-yanzu: Buhari bai ce dukkan matasan Najeriya malalata bane, yawancinsu yace – Fadar shugaban kasa ta yi fashin baki
Fadar shugaban kasa ta mayar da martini da maganan da yake yaduwa a kafofin sada llabarai musamman kafofin sada ra’ayi da zumunta cewa shugaba Muhammadu Buhari ya siffanta matasan Najeriya a matsayin rafkanannu cima zaune kuma malalata.
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Shugaba Buhari yayi kaca-kaca da Matasan Najeriya inda yace wasu ba su sa komai a gaba ba sai lalaci. Wannan magana ta Shugaban kasar ta fusata matasan kasar da Gwamnatin APC tayi wa alkawarin samawa aiki.
Wannan abu dai bai yiwa matasan Najeriya dadi ba inda har masoya shugaba Buharin suka koka da irin wannan furuci.
KU KARANTA: Matasa sun mayar da martani ga shugaba Buhari akan batun lalaci da cima zaune
Amma mai Magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki jawabi da yamman nan inda ya bayyana makasudin shugaba Buhari.
Yace: “ Yan adawa da masu juya Magana sun gaza fahimtar banbancin ‘yawancinsu’ da ‘dukkansu’. Ta yaya Kalmar ‘yawancinsu ‘ zai zama ‘dukkansu’, wannan rashin adalci ne.
Babu yadda shugaba Buhari a matsayin uban kasa wanda ke da yara matasa ya soki dukkan matasan Najeriya. Da ma yan adawa ne kawai kuma wannan siyasan rashin hankali ne.”
Legit.ng ta kawo muku cewa tsohon mataimakin shugaba kasa, Atiku Abubakar, ya nuna bacin ransa ga wannan furuci da shugaba Buhari yayi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng