Canjin kudade: Babban bankin kasa ya kara dala miliyan $210 cikin kasuwar hada-hadar kudaden kasar waje

Canjin kudade: Babban bankin kasa ya kara dala miliyan $210 cikin kasuwar hada-hadar kudaden kasar waje

- CBN na yunkurin dakile wahalar samun dala da tsada

- Bankin yace, zai cigaba da bayar da kudaden ga kasuwar hada-hadar kudaden domin tabbatar da daidaiton canjin

Babbban bankin kasa (CBN) ya kai dauki ga kasuwar hada-hadar kudaden ketare da zunzurutun kudaden da yakai dala miliyan $210 sakamakon karin bukatuwarsu, domin tabbatuwar daidaito a kasuwar canjin kudaden.

Canjin kudade: Babban bankin kasa ya kara dala miliyan $210 cikin kasuwar hada-hadar kudaden kasar waje
Canjin kudade: Babban bankin kasa ya kara dala miliyan $210 cikin kasuwar hada-hadar kudaden kasar waje

Wani lissafin al’kalumman dake bayanin kudaden da bankin na CBN ya tallafa da su, ya nuna cewa, bankin ya bayar da har $100m ga manyan dillalan canjin yayinda kuma aka baiwa kananan da matsakaitan yan canjin $55m kowannensu, domin samarwa da masu karatu da tafiya kasar waje dalar.

Da yake tabbatar da sakin kudaden, mukaddashin daraktan dake kula da sashin hulda da kamfanunuwa, Isaac Okorafor, ya bayyana cewa, sakin kudaden wani yanki na yunkurin da babban bankin yake yi na tabbatar da saisaita farashin canjin Naira da dala.

KU KARANTA: 'Yan kasuwar Kano na neman shiga Takun Saka da Hukumar Kwastam

Okorafor ya kuma kara da, CBN tayi murnar yadda harkokin canjin ke tafiya yanzu a kasuwar, sakamakon sabbin dokokin da ta bullo da su. Haka-zalika kuma bullo da zauren hulda tsakanin masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki ya taimaka mutuka wajen karuwar $20bn cikin kasuwar canjin kudaden tun bayan kirkirar zauren.

Sannan ya cigaba da bayyana cewa, babban bankin kasar ba zai saurara da shirin sa na tabbatar da daidaito kan yadda ake canzar da dalar ba.

Ko a Talatar da ta gabata dai sai da CBN din ya bayar da har $210m ga masu neman dalar a bisa dililai daban-daban.

Har dai ya zuwa ranar Laraba, ana cigaba da canzar da dalar ne a kasuwar canjin kudaden wajen kan $1 a matsayin Naira N360.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel