Asiri ya tonu: Bayan shekaru 18 wata mata ta gano Mijinta asiri yayi mata don ta so shi

Asiri ya tonu: Bayan shekaru 18 wata mata ta gano Mijinta asiri yayi mata don ta so shi

- Wata Mata ta bayyana yadda Mijinta ya sirce ta har ta zauna a gidansa daga kai masa ziyara

- Sai dai har ta haifa masa yaya shida, amma yanzu maganar na gaban al'kali domin yanke hukunci

- Mariam ta roki alkali da ya raba auren nasu don yanzu ba zata iya komawa ba

Bayan shekaru 18, wata mata mai suna Mariam adogoke ta roki kotu da ta taimaketa ta raba aurenta da Mijinta domin ta gano cewa asiri yayi mata har ya mallake ta.

Hakan kuwa ya faru ne a jiya Laraba a gaban wata kotu dake zamanta a garin Agodi na Ibadan a jihar Lagos, inda ta roki kotun da ta taimake ta ta raba auren nasu da mijin nata mai suna Lukman Adegoke, sakamakon yanzu asirin da yayi mata ya karya bata son shi.

Asiri ya tonu: Bayan shekaru 18 wata mata ta gano Mijinta asiri yayi mata don ta so shi
Asiri ya tonu: Bayan shekaru 18 wata mata ta gano Mijinta asiri yayi mata don ta so shi

Mariam ta shaidawa kotun cewa, “A shekarar 2000 taje gidan saurayin nata, kuma shiga dakin ke da wuya, sai hankali nay a gushe, tun daga nan bana son tafiya naje ko’ina. Haka na cigaba da zama a gidansa har tsawon shekaru uku sannan naje na ziyarci iyaye na”.

“Komawa ta gidan mahaifana ke da wuya, sai naji duk duniyar nan nafi son zama a gidan miji na, saboda haka kwana biyu kacal nayi a gidan iyaye na”.

Mariam ta bayyanawa kotun cewa,ta cigaba da zama a cikin yayain son nasa har zuwa yanzu da ta gano cewa ashe ta auri mijin da bai dace da it aba, sakamakon dawowa haiyacinta da tayi.

“Na haifa masa yaya shida amma biyu ne kawai ke raye, daya na waje na shima kuma ya rike daya”. ta fada

Daga karshe Mariam ta roki kotun da ta taimake ta ta raba auren nasu domin ba za ta sake iya zama da Mutumin da bata so ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng