Hukumar 'yan sanda ta gargadi mawakan gayu, ta basu shawarar

Hukumar 'yan sanda ta gargadi mawakan gayu, ta basu shawarar

- Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Legas, SP Chike Oti, ya yi kira ga mawakan Najeriya da su guji yin furucin daba da jagaliyanci a cikin wakokin su

- Kakakin ya bukaci mawakan da su zama masu koyi da mawakan mu na da dake amfani da waka wajen hada kan 'yan kasa da kiran a zauna lafiya

- Hukumar 'yan sanda shiyya ta II ta shirya wa mawaka taro domin ganin yadda za a iya amfani da wakokin wajen fadakar da matasa illolin dake tattare da aiyukan ta'addanci

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Legas, SP Chike Oti, ya yi kira ga mawakan Najeriya da su guji yin furucin daba da jagaliyanci a cikin wakokin su.

A wata ganawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), Oti, ya ce "ganin cewar mafi yawa daga cikin mawakan da muke da su matasa, akwai bukatar jan hankalin su a kan tasirin da kalaman su cikin wake kan iya yi ga ragowar matasa."

Mawakan gayu
Mawakan gayu

Kakakin ya bukaci mawakan da su zama masu koyi da mawakan mu na da dake amfani da waka wajen hada kan 'yan kasa da kiran a zauna lafiya.

DUBA WANNAN: Yadda jirgin sama dauke da gawar tsohon gwamna ya yi hatsari tare da hallaka mutum 13 a Legas

A wata hira daban da ta yi da NAN, kakakin hukumar 'yan sanda shiyyar ta II, Bodmus Dolapo, ta ce akwai bukatar daukan matakan da zasu dakile cusa akidar daba da aiyukan ta'addanci a zukatan matasan kasar nan.

Dolapo na wadannan kalamai ne yayin wani taro da hukumar 'yan sanda shiyya ta II ta shirya wa mawakan domin ganin yadda za a iya amfani da farin jinin da wakokin su ke da shi wajen fadakar da matasa illolin dake tattare da aiyukan ta'addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng