Karar kwana: Yan biki su 21 sun gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsari akan hanyar zuwa daurin aure

Karar kwana: Yan biki su 21 sun gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsari akan hanyar zuwa daurin aure

Rundunar Yansandan kasar Indiya ta sanar da mutuwar wasu matafiya su 21 dake kan hanyar halartar bikin daurin auren dan uwansu a yankin Indiya ta tsakiya, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hatsarin ya faru ne a lardin Madhya Pradesh, da yammacin ranar Talata 17 ga watan Afrilu, yayinda motar ta wuntsulo daga samar gada, inda ta afka cikin wani tafku busashshe.

KU KARANTA: Wani matashi ya yi ma Budurwarsa wanka da ruwan guba kan zarginta da neman maza

Wani babban jami’in Dansanda, Dilip Kumar ya bayyana cewa akalla mutane 29 sun jikkata ta hanyar samun rauni daban daban, inda yace da dama daga cikin wadanda abin ya shafa yan uwan Angon ne da suka nufi kauyen Pamari don daurin aurensa.

Karar kwana: Yan biki su 21 sun gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsari akan hanyar zuwa daurin aure
Motar daukan kaya

Kumar yace yan bikin sun cika wata motar daukan kaya ne makila, wanda ta kauce hanya a samar gadar Jogdaha, inda ta wuntsula wani tafki, tsawon takun kafa 60.

A wani mataki na nuna tausayi da jin kai, Ministan yankin Madhya Pradesh, Shivraj Chouhan ya sanar da bada tallafij dalan Amurka 3,044 ga yan uwan wadanda suka mutu, sai kuma dala 761 ga wadanda suka jikkata.

Dubun dubatan mutane ne suke mutuwa a hanyoyin kasar Indiya a kowanne shekara, sai dai yawanci an fi danganta hatsarin ga lalacewar hanyoyi, motoci marasa lafiya da kuma gangancin direbobi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng