Rikita-rikitar siyasa: Nayi nadamar taimakawa Buhari cin zaben 2015- Falae

Rikita-rikitar siyasa: Nayi nadamar taimakawa Buhari cin zaben 2015- Falae

- Wani wanda ya taimakawa Buhari cin zabe ya ce baya farin ciki da irin yadda abubuwa suke tafiya a mulkin Buhari

- Yace ko ba don rashin lafiyar Buhari ba ya kamata ya san cewa bai tabuka abin azo a gani ba

- Olu Falae, wanda shi ne shugaban jam'iyyar SDP ya bayyana hakan ne a ziyara da ya kaiwa Obasanjo

Shugaban jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) Chief Olu Falae, yace yayi da nasani kan goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2015, sakamakon gazawa da shugaban yayi wajen cika alkawarrukan da ya dauka yayin yakin neman zabe.

kuma a cewarsa, yayi tunanin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nuna halin dattako, ganin yadda abubuwa suke tafiya da kuma rashin lafiyarsa, yace ya hakura wani ya cigaba, sai baiyi hakan ba.

Olu Falae ya bayyana hakan ne ga manema labarai a garin Abeokuta bayan ya gana da tsohon sugaban kasa Olusegun Obasanjo. "Nazo tattaunawa ne da maigida na akan batutuwan da suka shafi siyasar kasar nan, domin lokacin yana shugaban kasa nayi aiki a karkashinsa a tsakanin 1977 da 1979".

Rikita-rikitar siyasa: Nayi nadamar taimakawa Buhari cin zaben 2015- FALAE
Rikita-rikitar siyasa: Nayi nadamar taimakawa Buhari cin zaben 2015- FALAE

"Duba da yadda abubuwa suke tafiya a kasar nan ne, naga ya dace nazo mu tattauna yadda zamu bayar da gudunmawarmu don cigaban Najeriya" Falae ya fada.

Ya kuma kara da cewa, alhakin gwamnati ne ta tabbatar ta samarwa Mutane tsaro, amma ni da ku da ita gwamnatin sun san ba su samar ba.

"Dukkanmu muna son canji kan yadda rashin aiki yake karuwa da kuma matsalar rashin tsaro da kullum kashe mutane ake, ga matsin tattalin arziki kara ta'azzara yake, Manoma yanzu tsoron zuwa gonarsu suke sakamakon rashin tsaro".

KU KARANTA: Dalilin da yasa Najeriya ke cikin damuwa - Tinubu

"Buhari abokina ne, kuma in baku manta ba na daga hannunsa yayinyakin neman zabe a filin wasa na Aamasingba a Ibadan na cewa Mutane su zabe shi, don ina tunanin abubuwa zasu canza Amma gaskiyar maganar ita ce, bai yi kokari yadda ya kamata ba".

Kuma Najeriya da yawa sun gaji da yadda abubuwa suke gudana, saboda haka kamar muna saukakawa Buharin ne ya gane hanyar da ta kamata ya bi shi da kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel