Yanzu-yanzu: Yan zanga-zanga sun kai farmaki majalisan dattawa, sun dauke sandar majalisa
Rikici ya barke a majalisar dattawa yanzun nan yayinda wasu yan zanga-zanga suka fasa majalisar kuma suka sace sandar doka.
Ana kyautata zaton cewa wadannan yan zanga-zanga magoya bayan sanatan da aka dakatar ne, Senata Ovie Omo-Agege.
Amma majalisar dattawa ta saki jawabi akan wannan abu da ya faru da safen nan, jawabin yace:
"A yau, wasu yan baranda karkashin jagorancin sanatan da aka dakatar, Ovie Omo-Agege, sun dira cikin majalisar dattawa suka sace sandar ikon majalisa"
"Wannan abu yakar kasa ne. Kuma wani yunkuri ne na juyin mulki ga wani reshen gwamnatin tarayya Najeriya. Dukkan hukumomin tsaro su tura jami'ansu domin tabbatar da cewa an dawo da sandar"
"Majalisa na ganawar gaggawa yanzu kuma zamu kawo muku cikakken rahoton anjima"
Kamar yadda kuka sani dai babu abinda majalisa zata iyayi ba tare da sandar nan na ajiye ba.
Wani rahoton idon shaida ya bayyana cewa yan baranda 5 ne suka shigo suka sace sandar da karfi da yaji kumu suka suburbudi mai tsaron sandan.
.
Zamu kawo muku cikakken rahoton.
Asali: Legit.ng