Ma'aikatan jihar Katsina sun shiga tasku har shida sun mutu sakamakon rashin biyan albashin watanni 26

Ma'aikatan jihar Katsina sun shiga tasku har shida sun mutu sakamakon rashin biyan albashin watanni 26

- Ma'aikatan kananan hukumomin jihar Katsina suna shiga tsaka mai wuya adalilin hana su albashinsu

- Sun kai kara kotin ma'aikata dake zamanta a Kano

- Kuma sun bukaci a biya diyyar Miliyoyin kudade bayan biya suk albashin nasu

Ma'aikata fiye da 610 daga ƙananan hukumomi 34 ne suke cikin ƙaƙa-na-kayi a dalilin hana su albashi gwamnatin Jihar Katsina tayi.

Bayanai dai sun nuna cewa, an riƙe albashin ma,'aikatan ne sakamakon ƙin zuwa tantancewa da gwannatin Jihar ta gudanar.

Mutane 6 daga cikin 610, sun mutum dalilin hana su albashin watanni 26 a Katsina

Mutane 6 daga cikin 610, sun mutum dalilin hana su albashin watanni 26 a Katsina

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, rayuwar ma'aikatan na cikin ƙunci sakamakon hana su albashin watanni har shida da aka yi, inda wasu ke fama da matsananciyar rashin lafiya ba tare da ƙudin sayen magani ba.

Maganar dai yanzu haka tana gaban kotun ma'aikata dake zamanta a Jihar Kano, kuma ba'a cimma matsaya tsakanin gwamnatin Katsinan da ma'iktan da bin ya shafa a zaman kotun na jiya ba.

Malam Aminu Ahmed, ɗayane daga cikin ma'aikatan da abin ya shafa, kuma ya shaida cewa, wasu daga cikinsu sun mutu sakamakon kuncin rashin albashin nasu.

"A yanzu da nake magana da ku, mutane shida daga cikinmu sun mutu sakamakon halin wahala da suka shiga a rashin biyansu albashin nasu domin suna da iyali kuma da albashin suka dogara". A cewar Ahmed.

KU KARANTA: Rikicin ‘Yan Shi’a: Kungiyar Amnesty ta fadawa gwamnatin tarayya cewa kada ta tauyewa yan Najeriya hakkinsu

Ya kuma kara da cewa, yawancin iyalan da abin ya shafa, yayansu sun daina zuwa makaranta sakamakon rashin iya biya da iyayen nasu basa yi.

Shi ma wani ma'akaici da yake a matakin albashi na 13, da yayi shekaru 17 yana aiki, yace, bai taba yin laifin da aka nemi ya bayar da ba'asi ba, sai yanzu kawai ba tare da wani kwakkwaran dalili ba aka daina biyansa.

Lamarin ya cefa rayuwarmu cikin mawuyacin hali "Albashi na bai taba wuce sati biyu ba'a biya ni ba, a tsawon shekaru 19 da ke aiki, amma yanzu watanni 26 kenan ba'a biya mu ba. Inji jibril Lawal Malumfashi".

Malumfashi ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya baki don ganin an samo bakin zare.

Lauyan ma'aikatan ya ce "laifin gwamnantin Jihar ne, saboda sunki yarda a sasanta maganar a wajen kotu kamar yadda muka tsara da farko". Kotun ta tsaida ranar 10 Mayu domin kawo rahotan karshe.

Ma'aikatan dai sun bukaci kotun ta sanya gwamnatin Jihar Katsinan ta biya su Naira Miliyan biyar (N500m) a matsayin kudaden matsalolin da suka cefa su bayan sun ta biya su albashin nasu.

Jaridar ta rawaito cewa, har yanzu gwamnatin Katsin bata kori mai'aikatan ba, suna nan a matsayinsu kuma suna duba yiwuwar biyan nasu bashin albashin nasu.

Shari'ar dai an fara ta ne tun a watan Oktobar shekarar da ta gabata a gaban mai shari'a E.D.E Isele, kuma lauya mai kare wadanda ake karar Barrister Kamaluddin Umar ya roki kotun da ta kori karar kurakuran da aka tabka yayin cike takardar shigar da karar, amma sai dai mai shari'ar bai karbi wannan roko na sa ba.

Mutane 6 daga cikin 610, sun mutum dalilin hana su albashin watanni 26 a Katsina

Mutane 6 daga cikin 610, sun mutum dalilin hana su albashin watanni 26 a Katsina
Source: UGC

Mai bawa gwamnan jihar Katsinan shawara kan harkokin mai'aikatan Alhaji Salisu Jibiya, cewa yayi,

"watakila rukunin ma'aikatan sun fada cikin wadanda ake zargi ne da zama ma'aikatan bogi da basu fito tantancewar ma'aikatan kananan hukumomin da aka gudanar ba". Amma gwamnatin Jihar da Majalisar dokokin Jihar sun kafa wani kwamiti da zai duba tare da nemo mafita ga lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel