Sojoji sun yiwa ƴan Boko Haram lugudan wuta a Maiduguri
- 'Yan Boko Haram sun ga takansu, Jiragen Sojojin sama Najeriya sun ragargaje su
- A wani harin baya-bayan nan da suka kai ranar Alhamis
Rundunar Sojin saman Najeriya ƙarƙashin atisayen Lafiya Dole ta ragargaji sansanin ƴan ta'addan Boko Haram.
Daraktan yaɗa labarai na rundunar ne AVM. Olatokunbo Adesanya ne ya tabbatar da kai harin a jiya Alhamis yau a Abuja.
Ya ce bayan bayanan sirri da jirginsu mara matuƙi ya samo ne na maɓoyar ƴan Boko Haram ne suka shirya kai harin. Kuma sun yi amfani da jirge biyu ne wajen kai harin.
KU KARANTA: An yi haka-haka a zaben Gwamnan Jihar Ekiti na 2014 - Buhari
Harin dai da Jiragen saman suka kai sansaninsu ƴan ta'addan mai nisan mil 13 a Arewa maso gabashin garin Bama. Kuma hotunan bayan kai harin sun nuna ya samu nasara sosai, sakamakon ruguza maɓoyar tasu da kuma fatattakarsu da su kayi.
A cewar Adesanya bayan kai harin ne daga baya Sojojin suka sake kai wani sabon hari kan wata maɓayar ƴan Boko Haram ɗin dake kilo-mita 15 a Arewa maso-kudu a ContiGobaran ta garin Gwoza.
A bisa wannan nasara ne rundunar Sojon saman ta yabawa jami'an nata dake cikin dakarun da suke taimakawa Atisayen Lafiya Dole ta sama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng