Jinjirin watan Sha'aban: Rikici na shirin kunno kai game da ranar fara azumi a Najeriya
Tun bayan da kafafen yada labarai suka ruwaito cewa Sarkin musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ayyana ranar Laraba, 18 ga watan Afrilu a matsayin 1 ga watan Sha'aban ne dai kawuna suka fara rarrabuwa game da ainahin sahihancin hakan.
KU KARANTA: Abu 5 da yakamata ku sani game da makwancin fiyayyen halitta
Wannan dai na kara fitowa fili ne biyo bayan jinjirin watan da jama'a da dama suka ayyana gani babba da har ma yakai kusan karfe 7:30 na dare bai fadi ba a ranar Talata 17 ga watan Afrilu.
Legit.ng ta samu cewa tuni dai wannan batun ya fara jawo cece-kuce a tsakanin musulman kasar inda suke ganin tabbas akwai lauje cikin nadi idan dai har masarautar ta dage kan cewa lallai a hakan za a tafi.
Wata mai alfarma dai na Ramadan da al'ummar musulmai ke yin azumi a cikin sa shine ke zuwa bayan watan Sha'aban wanda sabanin ganin watan sa kan shafi lokacin fara azumin da ma bukukuwan Sallah.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng